Wani jirgin soji ya yi hatsari a kasar Masar inda ya kashe mutu bakwai da ake cikinsa.
Helikwaftan ya rikito ne a yankin Sinai na kasar Masar a lokacin da yake dauke da sojoji da masu aikin sa ido na hadin gwiwa.
- Tsohon Shugaban Ghana Jerry Rawlings ya rasu
- Sojin Larabawa sun kakkabo jiragen ’yan Houthi a Saudiyya
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce wadanda suka mutun sun hada da Amurkawa biyar, Bafaranshe daya da kuma dan Jamhuriyar Czech.
Wata majiya a Isra’ila ta ce jami’an da hatsarin ya ritsa da na daga cikin rundunar wanzar da zaman lafiya da aka kafa tun a 1979.
Ta ce an kafa rundunar ce a lokacin da aka kulla yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Masar kuma ba ta da alaka da Majalisar Dinkin Duniya.