✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin saman Najeriya zai fara tashi kafin 29 ga watan Mayu – Gwamnati

Hadi Sirika, ya bayar da tabbacin a ranar Alhamis.

Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewar jirgin sama mallakin Najeriya na ‘Nigeria Air’ zai fara tashi kafin ranar 29 ga watan  Mayu, 2023.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, ne ya bayar da wannan tabbaci yayin taron masu ruwa da tsaki kan harkokin sufurin jiragen sama a ranar Alhamis.

Ya ce Gwamnatin Tarayya na daukar matakan da suka dace don shawo kan matsalolin da kamfanonin jiragen sama na ’yan asalin kasar nan suka bullo da su da suka je kotu domin dakatar da fara aikin jirgin.

Ministan, ya bayyana matakin da kamfanonin jiragen sama na cikin gida suka yi a matsayin rashin adalci, inda ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta tallafa wa kamfanonin jiragen sama fiye da sauran gwamnatocin baya.

Ya zarge su da kawo cikas ga tabbatar da kamfanin dillalai na kasa wanda zai yi tasiri wajen samar da ayyuka da damammaki a harkar.

Ya ce masana’antar sufurin jiragen sama ta Najeriya, ita ce daya tilo a duniya da ta ke da kwararrun matukan jirgi da ba su da aikin yi.

Ya ce ma’aikatan jirgin 50 ne suka zo wurinsa suna korafin rashin aikin yi, inda ya ce ya kamata ma’aikatan jirgin su kara daukar ma’aikata da kuma samar da wasu guraben ayyukan yi.

Ya ce kamfanin jiragen saman Ethiopian Airlines, wanda aka bai wa damar yin jigilar kayayyaki na kasa yana da kwarewa kuma yana samun riba sosai da zai kara kima a fannin sufurin jiragen sama na Najeriya.