✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin sama mai zuwa Isra’ila zai bi ta Saudiya a karon farko cikin shekara 70 – Netanyahu

Firayi Minsitan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya sanar da manema labarai cewa kasar Saudiyya ta bayar da dama ga jiragen sama masu zuwa Tel Abib su…

Firayi Minsitan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya sanar da manema labarai cewa kasar Saudiyya ta bayar da dama ga jiragen sama masu zuwa Tel Abib su wuce ta sararin samaniyar kasarta.

Ya fadi a lokacin da yake jawabi a birnin Washington DC, cewa “Jirgin saman Air Indiya ya sanya hannu a kwantiragin zuwa kasar Isra’ila ta kasar Saudiyya,” kamar yadda jaridar Times ta Israel ta ruwaito.

Kafin wannan sanarwar, kasar Saudiyya ta haramta duk wani jirgin sama mai tafiya zuwa kasar Isra’ila bi ta sararin samaniyarta a fiye da shekara 70 da suka gabata.  

A watan da jiya ne kamfanin sufurin jiragen sama na Air India ya tabbatar da cewa zai fara jigilar mutane daga Indiya zuwa Isra’ila mai sauri sosai sau uku a duk mako.

A lokacin da aka samu wannan sanarwar, wani jami’in Hukumar Jiragen Sama na kasar Isra’ila ya shaida wa Reuters cewa ba a fara wannan jigilar ba har zuwa farkon watan Maris.

A yanzu dai jirgin sama mallakar kasar Isra’ila na El Al ne kadai ke zuwa kasar Indiya kai-tsaye. Jiragen kuma suna yin zagaye ne ta yadda za su kauce wa kasar Saudiya, inda hakan ke kara wa tafiyar tsawon sa’a biyu.