An nemi wani karamin jirgin sama da ke dauke da fasinjoji 22 sama ko kasa an rasa a sararin samaniyar kasar Nepal ranar Lahadi.
Hukumomin kasar dai sun dakatar da binciken ala tilas sakamakon duhu yayin da ake ci gaba da fuskantar rashin tabbas kan makomar mutanen cikinsa.
Kakakin ’yan sandan kasar, Bishnu Kumar, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa duhun dare ya tilasta dakatar da neman jirgin, sai da safiyar Litinin aka ci gaba.
Jirgin, mallakin kamfanin sufurin jiragen sama na Tara Air dai na kan hanyarsa ce ta zuwa garin Jomsom, bayan ya taso daga birnin Pokhara mai nisan kilomita 200 daga birnin Kathmandu, babban birnin kasar.
Rahotanni sun ce jirgin ya bace ne jim kadan da tashinsa sama.
Har zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai kan inda jirgin yake ko makomar mutanen cikinsa, yayin da ake ci gaba da neman shi.
Kakakin kamfanin jirgin na Tata, Sudarshan Bartaula, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa akwai fasinjoji 19 da ma’aikatan jirgi uku a cikin jirgin.
Daga cikin mutanen da suke cikin jirgin dai shida ’yan kasashen waje ne; har da Indiyawa hudu da Jamusawa biyu.