✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin ruwa dauke da mutum 100 ya nutse a Kogin Binuwai

Wani jirgin ruwa ya kife a yayin da yake dauke da fasinjoji kimanin 100, yawancinsu kananan yara da mata a Kogin Binuwai. Fasinjojin da suka…

Wani jirgin ruwa ya kife a yayin da yake dauke da fasinjoji kimanin 100, yawancinsu kananan yara da mata a Kogin Binuwai.

Fasinjojin da suka hada da mata da kananan yara sun gamu da ibtila’in ne a hanyarsu ta komawa garin Binnari daga kasuwar Kifi ta Mayoreneyo da ke Karamar Hukumar Ardo-Kola ta Jihar Taraba.

Hatsarin ya auku ne kimanin mintoci 40 bayan kwalekwalen mai inji ya bar gabar ruwa ta Mayoreneyo da la’asar domin tsallaka Kogi Binuwai da ’yan kasuwar a ranar Asabar.

Wani mazaunin garin Mayoreneyo mai suna Musa Mayoreneyo ya shaida wa wakilinmu cewa jirgin da ya yi hatsarin ne ya kawo mutanen daga Mayoreneyo daga Binnari, a hanyarsa ta mayar da su gida.

Shi kuma wani dan garin Binnari, Malam Babangida Kwamnanda told ya hatsarin jirgin ruwan da yawancin fasinjojinsa mata da kananan yara ne, ya girgiza garin Binnari daga kauyukan da ke makwabtaka da shi.

Ya shaida wa wakilinmu ta waya “zuwa yanzu gawarwaki biyu aka gano.”

Wata majiya a gabar ruwa ta Mayoreneyo babu ko mutum daya da ke sanye da rigar kariya a lokacin da jirgin ya yi hatsari.

Amma Mukaddashin shugaban hukumar kula da koguna na cikin gida a Jihar Taraba, Jidda Mayoreneyo ya bayyana cewa bayyana cewa an gano gawarwakin mutum 15, daga cikin fasinjoji sama da 50 da jirgin ruwan ya yi hatsari da su.

Shugaban riko na Karamar Hukumar Ardo-Kola, Dalhatu Kawu ya bayyana cewa, “hatsarin jirgin ruwan ya auku ne a Binnari da ke Karamar Hukumar Karim-Lamido amma jirgin ya taso ne daga gabar ruwa ta Mayoreneyo.”

Kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, SP Usman  ya tabbatar da faruwar lamarin.