Jirgin farko na kamfanin jiragen sama na Najeriya Air, mallakin Gwamnatin Tarayya, wanda ta dade tana alkawarin zai fara aiki, yana hanyarsa ta zuwa Abuja daga kasar waje.
Aminiya ta gano cewa a safiyar Juma’a jirgin Nigeria Air ya fara lodi daga Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha zuwa Abuja, Babban Birnin Tarayya, kwana uku kafin saukar gwamnatin Shugaba Buhari da ta kafa kamfanin.
Ga bidiyon jirgin gabanin tashinsa zuwa Abuja.
’Yan Najeriya dai sun sha cewa sun gaji da gafara sa, ba su ga kaho ba, sakamakon alkawuran da gwamnatin ta sha yi na fara aikin jiragen Nigeria Air ba tare da hakan ya tabbata ba.
A yayin da gwamnatin Buhari ke shirin nade tabarmarta, Ministan Sufuri, Hadi Sirika, wanda ministan ya dauki gabarar kafa kamfanin, ya yi alkawarin jiragen za su fara tashi kafin gwamnatin ta mika mulki.
- An kama uba ya yi wa ’yarsa mai shekara 5 fyade
- Yadda dokar soke kayan lefe ta tayar da kura a Sakkwato
Da yake hira ta tashar talabijin na Channels, Hadi Sirika ya yi alkawarin cewa, “Ranar Juma’a jirgin Nigeria Air zai sauka a Najeriya domin ci gaba da gudanar da aiki.
“A ranar za a kaddamar da shi a Najeriysannan a kwaso sauran da suka rage.”
Kawo yanzu dai babu tabbacin ko nan take jiragen za su fara aikin jigilar fasinja, ko kuma za su takaita ne a aikin gwaji sai an cika sauran ka’idojojin sufurin jiragen sama kafin su fara aiki gadan-gadan.
Najeriya ta dade ba ta da kamfanin sufurin jiragen sama na kasa ba, sai a lokacin ministan, da ya dauki gabarar farfado da shi.
Sai dai tun a farkon shirin ya yi ta cikin karo da matsaloli da kuma adawa daga masu ruwa da tsaki, da ke ganin hakan ko dai barnar kudi ne, ko kuma ba a tsara shi yadda ya kamata ba.
A halin yanzu akwai karar da Kungiyar Masu Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (AON) ta shigar kotu tana neman a dakatar da jiragen kamfanin daga aiki.
Kungiyar ta shigar da karar ne tana kalubalantar tsarin rabon kason hanun jarin kamfanin na Nigeria Air.
Ko a ranar Alhamis kungiyar ta AON ta rubutta wa Shugaba Buhari wasika tana jan hankalinsa cewa kamfanin ba halastacce ba ne.