Mataimakin Gwamnan Borno, Umar Usman Kasafin da abokan tafiyarsa sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da suke ciki ya kama da wuta a sararin samaniya.
Injin jirgin Kamfanin Max Air ɗauke da mataimakin gwamnan da fasinjoji sama da 100 ya yi gobara ne jim bayan tashinsa da su daga filin jirgin sama na Muhammadu Buhari da ke Maiduguri.
Majiyarmu ta ce lamarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Talata, sakamakon wani abu da ake zargin tsuntsu ne ya shiga cikin injinan jirgin, ya yi sanadiyar tashin wutar.
A cewar wani ma’aikacin kamfanin jirgin Max Air, a sakamakon hakan ne jirgin ya yi saukar gaggawar a filin jirgin.
Ya ce kamfanin ya sake aika wani jirgi daga Kano domin jigilar fasinjojin da suka makale zuwa Abuja, yayin da wasu fasinjojin suka kwashe kayansu suka koma gida suka fasa tafiyar.
Jirgin da ya lalace ya ci gaba da tsayawa a filin jirgi na Maiduguri, ana gudanar da gyare-gyare yayin da hukumomi ke bincike a kan wannan lamari.
Masana harkokin sufurin jiragen sama sun bayyana damuwarsu game da yawaitar faruwar irin hakan da tsuntsaye ke haifarwa, wanda a cewarsu, babban kalubale ne da filayen jiragen Najeriya ke fuskanta.
Sun kuma yi kira da a inganta matakan tsaro a filayen jiragen saman.