✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin Kasan Kaduna-Abuja ya murkushe mota

Wani fasinja a jirgin ya ce bayan kade motar, jirgin ya ja motar har zuwa tasharsa da ke Kubwa kafin a fara aikin ceto

Jirgin Kasan Abuja-Kaduna ya kade wata mota a safiyar Alhamis a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna.

Wani fasinja a jirgin ya ce jirgin ya ja motar ya wuce da ita ne bayan direban motar ya yi kokarin tsallaka layin dogo a yayin da jirgin ya taho a guje.

Ya ce hatsarin ya auku ne kafin jirgin kasa ya isa Kubwa da ke yankin Babban Birnin Tarayya.

Kawo yanzu dai babu bayani ko an samu asarar rai ko na adadin mutanen da ke cikin motar.

Amma jirgin ya tsaya a tasharsa da ke Kubwa, inda jami’an tsaro ke kokarin cire motar da makale a jikinsa.

Ga hotunan wasu hotunan yadda abin ya faru: