✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin kasa ya yi hatsari a Abuja

Jirgin ya kaucewa hanyarsa ne a yankin Kubwa da ke Abuja.

Kasa da mako guda bayan da jirgin kasan Itakpe zuwa Warri ya kauce daga kan titinsa a Kogi, wani jirgin kuma a Yammacin ranar Juma’a ya yi hatsari a Abuja.

Ma’aikatar Jirgin Kasa reshen Abuja da Kaduna, ta tabbatar da faruwar lamarin a yankin Kubwa da ke Abuja, inda daruruwan fasinjoji da abin ya shafa suka yi cirko-cirko bayan jirgin ya sauka daga titinsa.

Kawo yanzu dai ba a san musabbabin abin da ya haddasa jirgin ba barin titin nasa ba, amma an ga fasinja da dama na mamakin yadda lamarin ya auku.

Shi ma Daraktan Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), Injiniya Fidet Okhiria, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya ce yana kokarin samun cikakken bayanai kan lamarin.

Idan dai za a tuna a ranar Lahadi ce wani jirgin kasa da ya taso daga Itakpe zuwa Warri ya kauce hanya a cikin daji a Jihar Kogi, amma an yi nasarar kwashe fasinjoji 143 da ke cikin jirgin.

Daga baya NRC ta rufe zirga-zirgar jirgin kasa yayin da aka fara aikin gyara hanyar nan take.

Hukumar ta ce tana zargin bata gari ne suka yi kokarin lalata titin jirgin, amma ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin don gano gaskiya.