An samu mutum guda da ya rasa ransa sakamakon wani hatsarin jirgin kasa da ya auku a kusa da birnin Makkah na Kasar Saudiyya.
Kafar Talabijin ta Arabiya ta ruwaito cewa, jirgin wanda mallakin Kamfanin Saudiyya da Spain SSTPC, ya yi taho mu gama ne tsakanin nisan kilomita 4 da tasharsa a garin Makkah.
- Zan kawo karshen rikicin Fulani da Makiyaya a Najeriya — Yariman Bakura
- Tsuntsun da ke zama kamar lema don farautar kifi
Bayanai sun ce hatsarin ya rutsa da mutumin da aka kashe ne yayin da yake tafiya kan titin jirgin.
Hukumomi sun yi kira ga mutane su rika nesa-nesa da titin jirgin kasa.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa,a shekarar 2018 ce aka kaddamar da jirgin mai gudaun tsiya domin jigila daga Makkah zuwa Madina, biranen da Masallatai mafi daraja ga muslumi suke a kasar.
Jirgin na Haramain Train shi ne mafi girman aikin sufuri da aka kaddamar baya bayan nan a kasar.