Mako guda bayan sake bude filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke Inug, har yanzu jiragen haya ba su fara sauka a filin ba.
A ranar 30 ga watan Agusta ne Gwamnatin Tarayya ta bude filin jirgin bayan yi masa kwaskwarima.
Kakakin Kamafin Jirgi na Air Peace wanda jirginsa zai fara sauka a filin, Stanley Olisa, ya tabbatar wa wakilinmu cewa kamfanin ya fara sayar da tikicin fasinjojin Inugu domin jigilarsu a ranar Laraba.
Tuni dama Kakakin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (NAMA), Henrieta Yakubu ta ce an an riga an fara cikakken harkokin zirga-zirgar fasinja a filin jirgin.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya bude filin jirgin washegarin ranar saukan jirgin farko bayan kammala gyara da fadada titin jirginsa da kuma sanya sabbin kayan kariya rayuka da sauran muhimman na’urori.
Ana sa ran saukar jirgin fasinja na farko a filin a ranar Laraba, duk da cewa wasu jiragen da suka yi jigilar manyan mutane da kuma gwajin sauka sun sauka da filin jiragen.