Daruruwan maniyyata Akin Hajji da suka fito daga Jihar Jigawa ne suka tsallake rijiya da baya sakamakon wata saukar gaggawa da jirginsu ya yi a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Jirgin wanda na Kamfanin Max Air ne mai lamba Max B747-HMM yana dauke da maniyyata 556 da suka tashi daga filin jirgin sama na Dutse a yammacin Laraba don sauke farali ya hadu da matsalar da ta sanya shi yin saukar gaggawa sakamakon ruwan sama da ake yi mai hade da kankara.
- Gwamnan Ribas ya rantsar da Kwamishinoni kwana 2 da shiga ofis
- ’Yan ta’addan ISWAP sun sace direbobi 4 a Borno
Hakan ya tilasta shi fasa tafiya kasar ta Saudiyya tare da juyowa Kano.
Majiyar Aminiya a filin na Malam Aminu Kano da ta nemi a boye sunanta ta cew a yanzu haka maniyyatan suna filin suna jiran a gyara jirgin.
“Gaskiya ne jirgi ya sauka anan Kano. A yanzu haka injiniyoyi suna kan gyaran jirgin wanda ya sami matsala daga gilashinsa. Da zarar an kammala gyaran za su ci gaba da tafiya,” in ji majiyar.
Wata maniyyaciyya da Aminiya ta tattauna da ita wacce kuma ta nemi a boye sunanta ta ce a yanzu haka suna zaune a cikin jirgi ana kokarin canza musu wani jirgin don ci gaba da tafiya.
A cewarta, matsalar ta afku ne sakamakon kankarar ruwan sama da ta bugi gilashin jirgin lamarin da ya janyo tsagewarsa.
“Mu dai ba mu ji faruwar komai ba sai aka sanar da mu cewa kankara ta bugi gilashin jirgin ya tsage don haka a yanzu za a juya da mu zuwa Kano don yin abin da ya dace. A yanzu haka Muna cikin jirgi sun shaida mana cewa za su canza mana wani jirgin don mu ci gaba da tafiya kasa mai tsarki”.