✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jiragen yaki Super Tucano 12 da Buhari ya sayo sun iso Najeriya

An tura jiragen zuwa yankin Arewa maso Gabas domin aikin samar da tsaro.

Karin jiragen yaki 12 samfurin Super Tucano da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sayo sun iso Najeriya.

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya sanar cewa jiragen su ne rukunin karshe na jiragen yakin da Gwamnatin Tarayya ta yi oda daga kasar Amurka a watannin baya.

“Jiragen yaki 12 samfurin Super Tucano da muke jira duk sun shigo hannunmu. Zuwa safiyar yau, an tura jiragen su 12 zuwa yankin Arewa maso Gabas,” inji ministan.

Gidan Rediyon Tarayya (FRCN), ya rawaito cewa Ministan ya sanar da hakan ne a wani shirin Talabijin da aka gudanar da shi a ranar Litinin.