✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiragen yaki sun ragargaji ’yan bindigar Kaduna

Jiragen soji sun yi wa ’yan bindiga ruwan wuta a Dajin Kadudu da na Kuyambana

Jiragen Rundunar Sojin Sama ta Najeriya sun tarwatsa sansanonin ’yan bindiga a Dajin Kuyambana da na Kuduru a Jihar Kaduna.

Rundunar Tsaro ta ce jiragen sun yi ruwan wuta a kan matattarar ’yan bindigar biyu ne a ranakun 2 da 3 ga Satumba, bayan samun bayanai a kansu.

Babban Jami’in Yada Labaran Runduna, Manjo Janar John Enenche, ya ce hare-haren jiragen yakin sun kashe ’yan bindigar da dama tare da rusa sansanoninsu da dazukan biyu.

Enenche ya ce an kai harin na Dajin Kuduru ne bayan jirgin sintiri ya hango taronn mutane dauke da bindigogi daf da wasu gidaje a cikin dajin.

Nan take aka tashi jiragen yaki suka yi raga-rage da wajen suka kuma kashe ’yan bindigar ko da ya ke bai fadi yawan wadanda aka kashe ba.

Ya ce a Dajin Kuyambana kuma jirgin yaki ya gano ’yan bindiga tare da shanun da suka sace a kusa da wata ruga, inda jiragen yaki suka yi ta musu dauki dai-dai.