✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiragen yaki ba za su iya kawar da ’yan bindiga ba —Farfesa Usman

Farfes Usman ya ce babu yadda za a yi a shawo kan matsalar fashin daji ta amfani da karfin soji

An bayyana cewa tura jiragen yaki na Super Tucano ko amfani da karfin soji ba za su yi tasiri wajen murkushe matsalar ’yan bindiga ba.

Tsohon Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Yusuf Usman, ya bayyana haka a wajen wani taro da kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta shirya don kawo karshen kalubalen da Fulani ke fuskanta a Najeriya.

“Akwai rawar da sojoji za su taka, amma babu yadda za a yi a shawo kan matsalar fashin daji a wannan kasa ta amfani da karfin soji,” inji shi.

Da yake gabatar da mukalarsa a wajen taron na ranar Alhamis mai taken ‘Makomar Fulani Makiyaya a Najeriya’, Farfesa Usman ya bayyana damuwarsa a kan abin da ya kira karfin soji da Gwamnatin Tarayya ke amfani da shi.

Usman ya yi wannan furuci ne bisa la’akari da jiragen yakin Tucano guda 12 da gwamnatin ta sayo ba da dadewa ba.

Matsalar zamantakewa

Ya ce matsalar ’yan fashin daji, matsala ce ta zamantakewa wadda ba za a iya magancewa ba ta hanyar da amfani da jiragen yaki.

“Fashin daji matsala ce ta zamantakewa kuma Najeriya na ci gaba da amfani da karfin soji don kawar da ita,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Sai mun hada kai baki dayanmu za mu iya kawar da matsalar; yanzu ba lokaci ne na dora laifi a kan juna ba, matsala ce da ta shafi kowannenmu.

“Sannan an kira sojoji su shigo su magance matsalar, na fada musu cewa sojoji ba za su iya wannan aikin ba.”

Haka nan, ya ce abubuwa biyu ne ke rura wutar wannan matsalar: shigo da miyagun kwayoyi daga Kudancin Najeriya da kuma shigo da makamai ta Arewanci Najeriya daga makwabtan kasashe kamar Jamhuriya Nijar.

Daga nan, ya tuno baya a lokacin da suka ziyarci ’yan fashin dajin a Kurmi tare da Sheikh Ahmad Gumi da sauransu, inda ya ce malamai na da rawar da za su taka wajen magance matsalar.

Tasirin malamai

“Turji ya yi zaman jiranmu na tsawon sa’a biyu, ya ce ya jira mu ne saboda ya samu labarin cewa malamai ne za su ziyarce su.

“Haka ma da muka tafi Jihar Neja, inda muka gana da jagorori shida na bangarorin ’yan fashin daga jihohin Arewa; a nan ma sun yi zaman jiran zuwanmu wanda haka ke nuni da irin girmamawar da suke yi wa malamai.

“Malamai da sarakuna ne ya kamata a yi amfani da su wajen jawo hankulan wadannan yara amma ba sojoji ba.

“Ya zama wajibi mu zauna mu yi nazari don gano inda muka aikata ba daidai ba.

“Daga Zamfara ba mu tsaya ko’ina ba sai Ilesha-Baruten da ke kusa da iyakar Jamhuriya Benin ko Jihar Kogi.

“Yadda muke karawa gaba, haka muka yi ta haduwa da Fulani cikin kyakkyawan yanayin da aka san su da shi rike da sandunansu na kiwo.

“Amma a Arewa, an musanya sandunan da bindiga kirar AK-47 da AK-49, sai ka tarar da kananan yara dauke da AK-47 da AK49,” inji shi.

Haka shi ma Sheikh Ahmad Gumi, ya nuna tsoronsa kan yadda mayakan Boko Haram suke tasiri a kan Fulani makiyaya.

Malamin ya jadadda matsayarsa cewa turar Najeriya ga Fulanin nan ta kai bango. Kana, ya koka kan yadda ake nuna wa Fulani kiyayya a kasar.

Ya kara da cewa, kashi 99 da cikin 100 na Fulani mutanen kirki ne, ’yan tsiraru daga cikinsu ne suka dau tafarkin aikata manyan laifuka.