✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jiragen soji sun tarwatsa maboyar ’yan ta’adda a Taraba

Jiragen yakin Najeriya sun tarwatsa maboyar ’yan ta'adda tare da kama bata-gari a Jihar Taraba.

Jiragen yakin Rundunar Sokin Sama ta Najeriya sun tarwatsa maboyar ’yan ta’adda a Jihar Taraba.

Jiragen sun ragargaza sansanonin ’yan ta’adda ne a kauyen Kambari da ke Karamar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar a inda sojojin suka kama da dama daga cikinsu.

Kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya shaida wa Aminya cewa, “Muna sane da aikin amma na sojojin sama ne kadai, ba mu da hurumin yin magana a kai.”

Wakilinmu ya nemi karin bayani daga kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, amma haka bai yiwu ba.

Majiyarmu ta shaida mana cewa yanzu kusan wata uku ke nan da ’yan ta’adda suka tare a yankin Kambari, suna sace mutane a kananan hukumomin Bali da Gassol da kuma Karim Lamido na Jihar Taraba.

Kawo yanzu kwana uku ke nan da sojoji ke gudanar da samame ta sama da kasa a yankin.

Sun kuma kama masu kai wa ’yan bindiga bayanai a kananan hukumomin Gassol da Karim Lamido masu makwabtakda da Kogin Binuwai.

Aminiya ta gano cewa sojoji sun yi kuskuren kashe wasu mutum uku a yankin Kwatan Nanido a Karama Hukumar Gassol.