Jiragen sojin Najeriya daga rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe ’yan ta’addan kungiyar ISWAP fiye da 100 a yankin marte da ke Jihar Borno.
Wata majiyar soji ta shaida wa Zagazola Makama cewa an kai harin ta sama ne a tsakiyar wannan wata na Oktoba 2023 a lokacin da ’yan ta’addan ke ganawa a dajin Bukar Mairam a Karamar Hukumar Marte.
- An kashe ’yar dan Majsliar Borno a gidan mijinta
- Shan maganin karfin maza ya maida magidanci abin kallo a gari
Ya ce “Dandalin ISR ya hango wani gagarumin motsi na ’yan tada kayar baya na tafiya zuwa wani wuri da ake zargin cibiyarsu ce, aka shammace su da ruwan bama-bomai ta sama aka yi kaca-kaca da su da abubuwan hawansu hade da makaman da ke tattatare da su.
Majiyar ta bayyana “’yan ta’addar sun shirya taro a yankin ne domin shirya kai hare-hare da daddare a kan wuraren da sojojin suke,” in ji majiyar.
Idan ba a manta ba, a ’yan kwanakin nan, ruwan bama-bamai da sojojin saman Najeriya suka yi da kuma aikin share fage da sojojin kasa suka yi, sun hallaka dimbin ’yan bindiga da ’yan ta’addar ISWAP a yankunan Arewa maso Gabas.