Jiragen eundunar sojin saman Najeriya sun kai wani hari a kan sansanin kungiyar ISWAP a yankin Dogon Chikun na jihar Borno a ranar Kirsimeti inda suka halaka akalla ’yan ta’adda 32.
A cewar wani kwararre kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, harin ya biyo bayan fadan cikin gida da kungiyar ta ISWAP ta yi.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, an kai harin ne a wani wuri da mayakan ISWAP suka sake haduwa bayan rikicin cikin gida da ya kai ga tarwatsewarsu.
Baya ga hasarar rayukan mutane da dama, an lalata dimbin makamai da wasu muhimman kayan aikin ’yan ta’addan a yayin farmakin.
Dogon Chikun dai wani yanki ne wanda ya shahara wajen ayyukan tada kayar baya, yana fuskantar sa ido sosai daga rundunar sojojin Najeriya saboda ayyukan ISWAP.
Rundunar sojojin Najeriya ta Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso Gabas na ci gaba da zafafa kai hare-hare kan ISWAP da Boko Haram, inda ta mayar da hankali wajen dakile ayyukansu da kuma kawar da babbar barazanar da suke yi.