✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jinjina da jiniyar jan jini

A daren karamin lauje da kofar hanci na watan Farin-birin shekarar dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, na yi fama da jinjina da…

A daren karamin lauje da kofar hanci na watan Farin-birin shekarar dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, na yi fama da jinjina da jiniyar jan jini da lange-lange mai ramar keta ya yi mini. Rabon da in yi artabu irin wannan da dan mitsitsin kwaron da ke shawagi cikin dare, tun a shekarar dubu karamin lauje da kwanciyar magirbi, lokacin da na sauka a unguwar Babban mutum mai rawanui da ke Jihar Bayan-kada. A wancan karon na koka, amma a wannan kuwa tabbas sai mun hada karfin karafan kwangiri wajen cin dunun mugu da dan muguwa.
Haurobiyawa lamarin dan tsito, mai tsikarar uwar jikin dan Adam cikin dare, ba karamar illa ba ce, domin a fadin duniya ana fama da nau’ukan jante da ke yi wa al’umma tarnaki, har su rika jan bante. Kai ni na taba ganin wanda aka sanya shi a turu, alhali ba a fasko cewa dan tsito ba ne ya tsikari kwanyarsa..
A lokacin da muke ’yan dugwi-dugwi, da zarar dan tsito ya yi shawagi a kan mu, har ya samu nazarar jan jinin mu, to ba za a dade ba, sai ka ga Inna da Baba sun yanke shawarar tafiya Farfajiyar Bokan Turai, idan kuwa suka jinkirta, sai mu yi ta fama da jante, mu yi ta jan bante, muna yi musu ruri. Da zarar an samu isa farfajiyar Bokan Turai, sai a duba mu, a dan tsira mana basilla, sannan  a hado mu da kuni; mu kuwa idan aka dura mana a baki, nan da nanmuke fara gunguni, saboda tsananin dacin kuni. Kai akwai lokacin da sai an makuren bakina nike yarda in kwankwadi maganin laulayin jante da jn bante, musamman ma idan na sha fate-fate.
’Yan makaranta, a shekara ta alif da manuniyar kasa da ta kasa da kwanciyar magirbi, na ziyarci kasar Sawun-diyyar Larabawa, da muka ziyarci birnin Manzo sai na bingire, nan da nan aka mika ni cikin Saidaliyya, inda aka jinka mini wani maganin jante “FEbERDOL.” Dan a murmure, sai na dawo birnin Makka al-mukarrama, nan ma aka karrama ni a farfajiyar Bokan turai, har Mai-duka ya kawo sauki.
Matsalar dan tsito, mai tsikarar gangar jiki, ya haifar wa al’umma laulayi, an saba ganin kamun ludayinsa a daukacin sassan duniya. Birtaniya ta hada lange-lange mai ramar keta da burtuntunar da ta burtuke shi, tamkar jarumin Baban-burin-huriyya, wato Barde Burutai. Su kuwa Asiyawa, wato kasashen da suka hada da Idon-isiya da Malalen-suya, har ma da Sinawa, duk yunkurawa wa suka yi wajen kirkira kwaro saumfurin lange-lange mai ramar keta, wand ake yin taho -mu-gama da dan tsito, su tsira masa tsitaka. Sannan sukan umarci daukacin al’ummarsu da su daina caba ado da bakaken suturu, ta yadda dan tsito ba zai sanya su a turu ba. Domin an ce cutar dan tsito in ta tattaba kwanya sai mutum ya shiga turu. Kasan kuwa, mutum ko dan gidan Maimotar roba ne ko Gizo-gizon-dakin-gwagggo, sai mu kai shi Dawanau ko Tsaunin Gwagware da ke birnin Dabo inda ba a dabo.
Akwai yankunan Asiya da dan tsito, lange-lange mai ramar keta ke sanya wa al’umarsu “ZAZZAbI DANGI,” wadda na ji a turancin Bokan Turai ana yi mata lakabi da “DENGUE FEbER.” Don haka suka ce kada aka wani ya caba ado da bakaken tufafi, musamman a cikin talatainin dare, har gara ka dauki hanyar zuwa Tumfafi, watakila ka samu tsira.
Masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan Farfajiya ta Dodorido, na fasko cewa, Haurobiyawa sun fara kokawa da ta’addancin dan tsito, lange-lange mai ramar keta, amma abin da suka kasa fahimta shi ne, tarin shirgin da muka jidge a juji da dagwaolon kwatami su suka haifar mana da JINJINA DA JAN JINANE, al’amarin da in ba mu yi sa’a ba, yana iya haifar da ZUkAR LUMANAR UWAR JIKI.
kasar Kyuba ma ta yunkura, inda \ta sanya kuba ta garkame kofarta, don kada lange-lange mai ramar keta ya kutso kai. Baya ga shirin garkame kofofin kan iyaka, har ma ta girke dakaru dubu manmuniyar kasa, don hana cuta zukar lumanar uwar jiki. Wannan dai darasi ne ga Haurobiyawa su yunkura wajen girke dakarun artabu da lange-lange mai ramar keta. Kodayake Bokayen turai da malaman jinya ya kamata su sa kafar wando guda da mugu dan muguwa, sannan duba gari, su zuba na-mujiya kan kowace maboyar nau’ukan kwaruka da ke illata rayuwar al’umma, don gudun kada su jefa mu cikin garari.
Haurobiyawa mu dauki darasi daga kasashen duniya, wadanda shugabannin al’umma suka himmatu ka’in da na’in wajen bai wa kowa da kowa kariyar, tunda kun dai i yadda Sinawa ke yin Bajintar birnin Beijin, ga Birtaniyawan da ba sacin Burtuntuna. Saboda haka mu rika share gefe-da-gwefen danger mu, musamman a wannan lokacin da jam’iyya mai maganin zogi da radadin ciwon kururungu ta zo da alamar tsintsiya. Lallai a yi kaimi wajen share kazanta, musamman jin cewa, malamai na karanta wa almajirai cewa, Fiyayyen halitta ya ce tsafta yanki ne na imani. Ita kuwa Gwmanatin Haurobiya akwai bukatar ta dawo da aikin DUBA GARI, don gudun kada al’umma ta shiga cikin GARARI.
Da zarar Baban-burin-huriyya yi dawo daga balaguron da ya yi zuwa kasar Sawun-diyyar Larabawa, tabbas zan yi kokarin kai kukan Haurobiyawa kan irin ta’addancin da lange-lange mai ramar keta ke yi wa al’umma a lokacin zafi. Duk da haka kafin baban mu ya dawo sai mu yi yunkurin nusar da Usainin-Babajo ko zai iya dan tagazawa wajen kwatanta dabarun ingiza keyar dan tsito ya daina cutar Haurobiyawa. Kafin dai jagororin al’umma su dauki mataki, ina ganin akwai bukatar mu kunna wayar leko, mu fesa maganin kwari, sannan mu kullube a cikin raga, ta yadda za mu yi raga-raga da dan mitsitsin kwaron da ke yi mana jinjina da jiniyar jan jini. Domin a halin yanzu al’ummar duniya dan tsito yana yi mata SARMA-SARMA DIF-DIF, wato irin karar takun dodanni, musamman jin cewa, shi ne jigo jajjabo cutar ZUkAR LUMANAR gangar jiki, wadda ta bazu a kasar BARAZANA-DA-ZILLIYA, inda ake takama da tamola, amma suna fama da dan mitsitsi mai mautsuttsuke garkuwar jiki.