Saboda haka ne, Allah Ya siffanta malamai da tsoron Allah, Ya ce, “Kuma daga mutane da dabbobi da bisashen gida, masu sabanin launinsu, kamar wancan. Malamai kawai ke tsoron Allah daga cikin bayinSa. Lallai Allah Mabuwayi ne, Mai gafara.” (k:35:28). Hakika malamai sun cisgo tsoron Allah ne sakamakon iliminsu na sanin cewa Allah ne Mammallakin duniya, Shi ke da mulkin abin da ke cikin sama da kasa, zuwa gare Shi dukkan al’amura suke komawa, Shi ne Mai juya al’amuran dukkan halitta, Shi ne Rayayye Wanda ba Ya mutuwa, Madauwami da daukacin halitta ke jingina gare Shi, gare Shi halitta take neman komai, sabanin waninSa, wanda gajiyayye ne da bai iya mallaka wa kansa amfani ko tunkude cuta, ko mutuwa ko rayuwa ko tashi!
Abin sani halittu gaba daya, suna iya zama sanadi ne kawai na iyar da abin da Allah Ya hukunta, ko Ya kaddara ga mutum, kamar yadda bayanin haka ya zo cikin Hadisin da Tirmizi ya ruwaito a cikin Jami’i dinsa, Imam Ahmad a Musnad, sai Hakim a Mustadrik da isnadi ingantacce -kuma lafazi mai zuwa na Tirmizi ne- daga Abdullahi dan Abbas (RA), cewa “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ya kai yaro! In sanar da kai wasu kalmomi mana: Ka kiyaye Allah, sai Ya kiyaye ka, ka kiyaye Allah za ka same Shi a gabanka. Idan za ka roka ka roki Allah, kuma idan za ka nemi taimako ka nemi taimakon Allah. Ka sani da al’umma gaba daya za ta hadu a kan ta amfane ka, ba za ta amfane ka da komai ba, sai da abin da Allah Ya hukunta a kanka, kuma da za ta hadu a kan ta cutar da kai, ba za ta iya cutar da kai da komai ba, sai da abin da Allah Ya hukunta a kanka. An dage alkaluma, kuma takardu sun bushe!”
Ya ku bayin Allah! Ba wai muna nufin tsurar tsoro kawai ba ne, a’a muna nufin wani al’amari na daban ne, wato ya zamo sila ko hanya, ba wai iyakar tukewa ko manufa ba, don wannan yana iya gushewa da gushewar abin da ake tsoro, wannan ya sa halin ’yan Aljanna shi ne su babu tsoro a kansu, kuma ba su bakin ciki a cikinta, saboda gushewar tsoron fada wa ukuba tare da samun gidan daraja da lada, falala daga Allah Madaukaki da girmamawa daga gare Shi, sakamakon hakurinsu bisa da’a da saunarsu ga aikata sabo, saboda haka tsoro ya kasance abin godiya mai gaskatawa-kamar yadda wani malami ya ce- tsoro shi ne abin da ke shiga tsakanin ma’abucinsa da abin da Allah Ya haramta, idan ya wuce haka, ana tsoron a samu yanke kauna wanda Allah Ya yi hani a kansa, Yana mai bayyana shi a matsayin daya daga cikin siffofin kafirai, Madaukaki Ya ce, “Babu mai yanke kauna daga rahamar Allah face, mutanen nan kafirai.” (k:12:87).
Wani malami ya ce, “Zuciya a yayin tafiyarta ga Allah Madaukaki,kamar tsuntsu take, so ne kanta, tsoro da kwadayi fika-fikanta, idan kai da fika-fikai suka zama lafiyayyu, sai tsuntsu ya kyautata tashi, idan kuma aka yanke kai, sai tsuntsun ya mutu, idan aka rasa fika-fikai kuma duk lokacin da ya yunkura sai ya tuntsure. Sai dai magabata na kwarai sun fi son a karfafa ingancin fiffiken kwadayi a kan fiffiken tsoro, kuma a yayin barin duniya, mutum ya karfafa fiffiken kwadayin rahama a kan fiffiken tsoro. Kuma mafi kamalar halaye shi ne, a daidaita kwadayi da tsoro tare da bayar da galaba a kan so, domin so shi ne kwaranga, kwadayi kuma matakala, sannan tsoro igiyar da ake rikewa a kai ga Allah Mai yawan kyauta da karimci.”
Ku saurara! Daga cikin mafiya girman abin da ya kamata a mayar da hankali a kai, a lura da shi lura na hakika, a yi kokari a zage dantse don samunsa, shi ne tarbiyyantar da zuciya a kan son Ubangiji Madaukaki da jin tsoronSa da kwadayin rahamarSa tare da karfin imani da Shi, a karfafa tauhidi a RububiyyarSa da UluhiyyarSa da SiffofinSa, a ilimantu a san abin da Ya yi tattali ga masu tsoronSa a Aljanna na daga ni’imomi matabbata da kuma abin da ya tanada ga masu saba maSa na daga ukuba da azaba mai radadi. A tarbiyyantar da rai da zukata kan tabbata wajen yi wa kai hisabi, domin a hana su bin sha’awoyinsu da tsayar da su a kan hanyar kwarai da gaskiya da kange su daga fada wa karya da zalunci ta kowace fuska da kama.
Ina neman tsarin Allah daga Shaidan jefaffe (la’ananne). “Lallai ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske, Annabawa wadanda suke sun sallama, suna yin hukunci da ita ga wadanda suka tuba (Yahudu), da malaman tarbiyya da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Liffafin Allah, kuma sun kasance a kansa, masu ba da shaida. To, kada ku ji tsoron mutane, ku ji tsoroNa, kuma kada ku sayi ’yan kudi kadan da ayoyiNa. Wanda bai yi hukunci ba da abin Allah Ya saukar, to, wadannan su ne kafirai.” (k:5:44).
Allah Ya amfanar da ni da ku da shiriyar LittafinSa da Sunnar AnnabinSa. Ina fadin haka, ina neman gafarar Allah Mai girma a gare ni da ku daga dukkan zunubi, lallai Shi Mai yawan gafara ne Mai jinkai.
Huduba ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah Majibincin Salihai, ina gode maSa Madaukaki. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, kuma ina shaidawa lallai Shugabanmu kuma Manzonmu Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa, Shugaban Manzanni, kuma jagoran mafiya alherin mutane. Ya Allah Ka kara tsira da aminci a bisa bawanKa kuma ManzonKa Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya, da tabi’ai da masu bin su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Wani malami ya ce: “Duk wanda ka ji tsoronsa gudu kake daga gare shi, ban da Allah Madaukaki. Shi idan ka ji tsoronSa gudu kake yi ka koma wurinSa, don haka mai tsoron Allah gudu yake daga Ubangijinsa zuwa ga Ubangijinsa, mai nufatar Ubangijinsa ne, domin ya san babu matsera, babu mafaka daga Allah sai a wurin Allah. Kuma jin tsoronSa yana haifar da samuwar amincewa, saboda haka kan haifar da tsarkake aiki da kyautata shi da bin koyarwar Manzon Allah (SAW), da tsoron saba wa umurninSa (SWT).