Jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara sun nuna gamsuwarsu kan yadda da tsarin tarayya da ake tafiya a kansa tare da kiran a ci gaba da tafiyar da shi ba tare da yi masa gyaran fuska ba. Sai dai sun ce akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta mayar da wasu fannonin rayuwa ga jihohi don tafiyar da su kamar sha’anin kiwon lafiya da sufuri da kashe gobara, ita kuma ta mayar da hankali a kan tsaro da harkokin kasashen waje da kudin kasa.
Wannan ne matsayar da jihohin suka gabatar a taron kwamitin duba fasalin kasa da aka gudanar a Makarantar Haddar kur’ani ta Sarkin Musulmi Maccido da ke Sakkwato a ranar Litinin da ta gabata.
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Chiso Abdullahi Dattijo ya gabatar da matsayar, inda ya ce jihohin ba su yarda rage ikon gwamnatin tsakiya ba, kuma ba su yarda a kirkiro ko a hade wata jiha a kasar nan ba.
Kan rabon arzikin kasa kuwa Jihar Sakkwato ta nemi a duba lamarin, ta yadda Gwamnatin Tarayya za ta rika amfana da kashi 45, jihohi da kashi 35 kananan hukumomi da 22. Sai dai Jihar Kebbi tana son rabon ya koma kashi 40 na tarayya, 40 na jihohi, 20 na kananan hukumomi.
Haka Sakkwato ta amince a bai wa kananan hukumomi cin gashin kansu amma jihohi su rika sanya musu ido, kuma ta yarda a rika tsayar da dan takara mai cin gashin kansa, yayin da Kebbi ta shure hakan.
Jihar Zamfara ta amince a ci gaba da tafiya kamar yadda ake cikin yanzu, kada a yi wani sauyi ko canji a dukan jagorancin gwamnati.
Shugaban Kwamitin, kuma Gwamnan Filato Mista Simon Lalong ya tabbatar wa jihohin uku cewa zai mika duk abin da suka fada ga uwar jam’iyya ta kasa ba tare da bata lokaci ko canja abin da suka ce ba.
A bayanan Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da na Kebbi Alhaji Atiku Bagudu da na Zamfara wanda Mataimakinsa Malam Ibrahim Wakala ya wakilta sun ce an shirya taron ne da zimmar jin ra’ayoyin mutane kan sake fasalin kasa da jam’iyyarsu ta APC ta shirya domin ta san hakikanin gaskiyar ra’ayin jama’ar kasar nan.