Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano jihohi 30 na kasar nan sun samu kudin shigar da zai iya magance daya cikin kashi uku na matsalolin albashi da alawus na ma’aikatansu ne kawai.
Alkalman da Cibiyar Kididdiga ta Kasa ta wallafa sun nuna cewa a shekarar 2016 jihohi 30 da hukumar ta yi nazarinsu banda jihar Legas sun samu kudin shiga a jihohinsu da ya kai kimanin Naira biliyan 515 da digo 16 wanda shi ne kashi daya bisa uku na Naira tiriliyan 1 da digo 479 da jihohin suka kashe kan hakkokin ma’aikatansu a shekarar.
Hakkokin ma’aikatan sun hada da albashi da fansho da garatutin ma’aikata na jihohin da na kanana hukumomi.
Halin tsaka-mai-wuya da jihohin da suka samu kansu na karancin kudi ya sanya jihohin da wuya suke biyan albashin ma’aikatansu ba a ma batun gudanar da manyan ayyuka.