Gwamnatin Jihar Katsina za ta tallafa wa nakasassu domin su yi dogaro da kansu maimakon yawon barace-barace.
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ne ya shaida haka a Talatar makon jiya yayin da ya karbi bakuncin kungiyar ‘yan wasa Guragu mai suna ‘PARA SOCCER’ a gidan gwamnatin jihar a lokacin da suka kai masa ziyara tare kuma da gabatar masa da kofuffukan da kungiyar ta ciwo a wasanni dabam-daban da ta yi a gida da kuma waje.
Gwamna Masari ya ce,”bara kaskanci ce ga rayuwarmu musamman ga nakasassu wadanda suke ganin kamar ita kadai ce hanyar rayuwa”.
Gwamna Masari ya tunatar da nakasassu tarihin shahararen marubucin nan marigayi Aliyu Namangi wanda ya ce da makanta aka haife shi amma sai ga shi har gobe ana anfana da gudunmuwar da ya bayar ta hanyar rubuta wannan littafi na Infiraji. “Wannan littafi na Infiraji ga shi har gobe yana amfanar da mu, saboda wa’azin da ke cikinsa.
Kun ga bai bari wannan tunani na nakasa ya mamaye masa zuciya da har zai fada bara ba”.
Gwamna Masari wanda bayan nuna farin cikinsa musamman akan cin wannan kofi na wasannin guragun da aka yi a kasar Ghana inda kungiyar wasan ta PARA SOCCER da ke jihar wadda ta wakilci Najeriya ta ciwo kofin, akan haka ne gwamnan ya amsa dukkan rokon da kungiyar ta yi masa.
Daga cikin rokon da shugaban kungiyar ya yi sun hada da sama wa ‘yan kungiyar abin hawa (mota) da kuma filin da za su rika yin wasa, inda Gwamna Masari ya kara har da kayan wasa da kuma ganin an tallafa masu domin dogaro da kansu.
Tun farko sai da shugaban kungiyar Mai shari’a Musa dalladi ya shaidawa Gwamna Masari irin nasarorin da kungiyar ta samu a wasannin da ta yi a baya. “Akwai gasar Baba Mai Mangwaro wadda aka yi a Yola Adamawa mun zo na 4, kazalika akwai wasan da aka yi na Arewa maso Yamma nan ma mun zo na biyu da sauran wasanni. Yau ga shi mun dauko kofi daga kasar Ghana. A nan ina so in yi amfani da wannan dama domin in roki mai girma Gwamna da ya sama wa wadannan ‘yan wasa abin hawa da filin wasa saboda a yanzu filin aro ne suke amfani da shi”.
Jihar Katsina za ta saka wa nakasassun ’yan wasa da alheri
Gwamnatin Jihar Katsina za ta tallafa wa nakasassu domin su yi dogaro da kansu maimakon yawon barace-barace. Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ne…