✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Katsina ta kashe N175.5m wajen gyaran filayen wasanni 

Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta kashe zunzurutun kudi har Naira miliyan 175.5 wajen gyara filayen wasanni guda biyu a jihar.

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta kashe Naira miliyan 175.5 wajen gyara filayen wasanni guda biyu a jihar.

Kwamishinan Wasannin jihar, Sani Danlami ne ya bayyana haka yayin da yake bayyana nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a ranar Laraba.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta kashe Naira miliyan 111.3 wajen gyaran filin wasa na cikin garin Malumfashi, sai kuma Naira miliyan 64.2 wajen gyaran filin wasa da ke cikin garin Katsina.

Sani ya kara da cewa gwamnati ta yi hakan ne domin farfado da harkokin wasanni a jihar.

Kazalika, ya ce ma’aikatar ta kuma kashe Naira miliyan 9.25 wajen kwashe masu larurar tabin hankali da ke gararamba a kan titunan jihar, sai miliyan 1.57 da aka yi amfani da su wajen mayar da masu gudun hijira zuwa garuruwansu da ke ciki da wajen jihar.