Jihar Gombe ta shiga jerin jihohin da za su fafata a wasannin gasar nakasassu ta kasa irinta ta farko a matakin kasa da za a gudanar a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Jihar ta ce za a fafata da ita a dukkan nau’i shida na gasar.
- Ahmed Lawan ya roki ’yan Najeriya su sake ba APC dama a 2023
- ’Yan bola jari sun zargi ma’aikata da kone dukiyarsu ta N70m a Ogun
Da yake yi wa ’yan wasan jawabi kafin su bar Gombe, Shugaban Hukumar wasanni ta jihar, Mista Olanre Daniel, gargadin su ya yi da cewa su zama jakadu na gari masu kiyaye dokokin da aka shimfida musu yayin gasar.
Shugaban ya kuma gode wa Gwamnan Jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa amincewa da ba su dama su shiga a fafata da su a gasar.
Ya kuma gargadi ’yan wasan da cewa ba kallon gari za su je ba, za su je ne don ciyo wa Jihar azurfa da tagulla.
Olanre, ya tabbatar wa da ’yan wasan cewa suna da goyon bayan gwamnati har a kammala gasar.
Wasannin da za su shiga a fafata da su din sun hada da kwallon guragu, da kwallon nakasassu da na kurame da na masu daga karfe da wasan tsere na guragu da dai sauransu.