Mukaddashin Babban Sufeton ’Yan Sanda mai kula da shiya ta 12 da, AIG Audu Adamu Madaki ya bayyana Jihar Gombe a matsayin wacce ta taka rawar gani wajen dakile ayyukan ’yan ta’adda.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wa Gwamnan Jihar, Inuwa Yahaya ziyara ta musamman a ofishinsa da nufin karfafa alaka ta yadda za a magance matsalolin tsaro.
- Fulani sun fi kowa shan wahalar masu garkuwa da mutane – Bagudu
- Abin da ya sa sai yanzu Buhari ya fara sauya ministoci
AIG Audu, ya ce za su kara bai wa gwamnatin Jihar cikakken hadin kai da goyon baya wajen taimakawa a kara magance matsalar ta tsaro a fadin Jihar.
Mukaddashin Babban Sufeton ya kuma yaba wa Gwamnan bisa daukar kwararan matakai wajen magance matsalolin tsaro a Jihar da irin goyon bayan da yake bai wa ’yan sanda da sauran jami’an tsaro.
Da yake nasa jawabin, Gwamna Yahaya ya bayyana cewa aikin dan sanda aiki ne mai daraja ba ga gwamnati kadai ba har a tsakanin al’umma saboda kokarin su kullum na ganin an wanzar da zaman lafiya da tsaro.
Gwamnan yace saboda yadda gwamnatin sa ke bai wa harkar tsaron al’umma muhimmanci ya sa ta kirkiro da Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Inganta Tarbiyya da nufin samun ingantacciyar hulda tsakanin al’umma da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
A cewar Gwamnan, kalubalen tsaron Jihar na da yawa saboda kasancewarta a tsakiyar jihohin Arewa maso Gabas, wanda hakan ya sanya ta zama matattarar ’yan gudun hijira daga Jihohin Borno da Yobe da ma Adamawa saboda yanayin zaman lafiya da ake da shi a cikinta.