Yara kimanin miliyan biyu ne ba sa zuwa makaranta a Jihar Zamfara, daga cikin yara fiye da miliyan 10 marasa halartar makaranta a Najeriya.
Hakan ta sa gwamnatin jihar bullo da shirin sanya ilimin boko a tsarin makarantun allo da kuma ciyar da almajirai a makarantun.
Manufar shirin ita ce, ”Ba wa wadannan yara damar lakantar ilimin dukkanin bangarorin biyu, da kuma dakile matsalar barace-barace”, a cewar hukumar ilimin bai daya ta jihar.
Shugaban hukumar Abubakar Aliyu Maradun ya kara da cewa za a fara shirin ne yara 30,000 a makarantu 280 daga a kananan hukumomi takwas.
Ya ce ”An tanadi kayayyakin karatu, littattafan yara da kuma malaman, sannan muna ba su abinci sau daya a kullum”.
Jihar ta gano girmar matsalar yaran marasa zuwa makaranta ne bayan alkaluman da a baya suka nuna cewa yara miliyan daya ne a jihar ba sa zuwa makaranta.
Zamfara na daga jihohin da matsalar tsaro ta yi kamari, sakamakon hare-haren ’yan bindiga.
Ayyukan bindiga a jihar sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama baya ga tilasta wa dubbai tserewa daga gidajensu.