Wani jigo a jam’iyyar APC a garin Danko Wasagu ta jihar Kebbi, Alhaji Dan Musa Ribah ya fice daga jam’iyyar ya koma jam’iyyar adawa ta PDP tare da mabiyansa.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kebbi Alhaji Haruna Saidu ne ya bayyana hakan a garin Ribah da ke karamar hukumar Danko Wasagu ta jihar lokacin da yake karbar masu canza shekar a karshen mako.