Maimakon auren zawarawa da wadansu gwamnoni suke yi a jihohinsu, a Jihar Jigawa Gwamna Badaru Abubakar yana yi wa marayu aure ne da nufin tallafa wa marasa galifu a jihar.
Mafiya yawan marayun da aka daura wa auren masu karancin shekaru ne wanda hakan ne ya sanya Mai martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammed Sunusi ya bukaci wadanda aka daurawa aure da marayun su bar su kummala makaranta, domin su samu ilimin addini da na zamani, inda a cewarsa yin hakan zai taimaka wa marayun wajen sanin yadda za su bauta wa Allah da kuma ita kanta rayuwar auren.
An yi bikin daurin auren marayu 270 a ranar Asabar din ta gabata a Babban Masallacin Dutse, wadanda aka zakulo su daga Masarautar Dutse, kuma a kowace mazabar akwatin siyasa aka dauko yarinya daya.
Alhaji Nuhu Sunusi ya kara da cewa su ne suka yi amfani da masu unguwanni tare da taimakon ’yan Hisba wajen zakulo marayun, sannan masarautar ta tantance su.
Sarkin ya kara da cewa kowace karamar hukumar ta aurar da marayu 10 ne wadansu 11, ya danganta da yawan akwatunansu na siyasa, amma dai yara 270 aka daura wa auren.
Sarkin ya bukaci wadanda suka auri marayun su zauna da su lafiya kuma su rike su amana, kuma an daura auren nasu ne a kan sadaki Naira dubu 20 kowacce.
Da yake jawabi a taron, Mai ba Gwamnan Jihar Jigawa Shawara kan Harkokin Addini, Mujitafa Sale Kwalam, ya ce Gwamnatin Jihar ta ware Naira miliyan 94 don yi wa marayun kayan daki masu nagarta da daraja.
Ya ja kunnen shugabannin kananan hukumomin jihar cewa su tsaya su yi wa yaran kayan dakin da aka ba su a rubuce. Ya kara da cewa duk wanda aka ba ta kayan da ba su cika ba, wakilanta su gaggauta sanar da gwamnati ta hanyar Hisba da ke kananan hukumominsu.
Ya ce duk wanda ya ki bin umarnin da aka ba shi a kan kayan dakin marayun, babu makawa za a dauki mataki a kansa.