Jiga-jigan jam’iyyar PDP wadanda suka hada da ’yan takarar Gwamna da na majalisar kasa tare da majalisar jiha a jihar Taraba ne ke yinkurin canja sheka zuwa wata jam’iyyar saboda rashin adalci da suka ce uwar jam’iyyar ta yi musu.
Jiga jigan jamiyyar PDP da ke yin wannan barazanar, sun hada da Mista Dabid Sabo Kente da sanata Abubakar Tutare, tare da dubban magoya bayan tsohon mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Garba Umar. Binciken da wakilinmu ya gudanar, ya nuna cewa kin gudanar da zaben fitar da ’yan takara na mukamai daban-daban, wadanda suka hada da na Gwamna da uwar jam’iyyar ta yi shi, ya harzuka ’yan jam’iyyar yin wannan barazana.
Wani daga cikin wakilin da ya kamata su zabi ’yan takarar, wadanda uwar jam’iyyar ta tilasta wa zuwa Garin Abuja, mutmin mai suna Musa Yakubu ya shaida wa wakilinmu cewa, su sama da 400 suka isa Abuja da tsammanin cewa za a gudanar da zaben fitar da ’yan takara, ta hanyar gaskiya kamar yadda dokokin jam’iyyar suka tanadar, amma da suka isa hedkwatar jam’iyyar a Abuja sai magana ta canja.
A cewarsa, sun iske kofar shiga sakatariyyar PDP a rufe a lokaci da suka isa Abuja, inda masu gadi suka tambayesu inda suka fito. Musa Yakubu ya ce sun shaida wa masu gadin sakatariyar cewa su wakilai ne daga Jihar Taraba kuma an umurce su zuwa ofishin ne don gudanar da zabe fitar da ’yan takara. Mallam Musa Yakubu ya ce, an hana su shiga cikin sakatariyar jam’iyyar.
Ya ce wani daga cikin manyan jam’iyyar ya fito daga cikin ofishin jam’iyyar rike da wata takarda a hannunsa, inda ya ce kowa ya saurara ya ji sunayen da zai kira, kuma duk wanda bai ji sunan sa ba, to ya yi maza-maza ya bar wurin.
Ya kara da cewa ana cikin kiran sunayen sai manyan motoci dauke da sojoji da ’yan sandan kwantar da tarzoma suka iso sakatariyar jam’iyyar. A cewar sa, sunayen da aka kira sun sha bam ban da sunayen su,watau wakilai da aka zaba don gudanar da zaben fitar da ’yan takara.
Ya ce jami’an tsaron da aka turo wurin sun umurci dukkan wanda bai ji sunansa ba da su bar wurin maza-maza.
Mallam Musa Yakubu ya ce wannan lamari ya ba su mamaki, kuma wadannan sunaye da aka kira ba su ne wadanda aka zaba a lokacin zabukan wakilai da aka gudanar a duk fadin jihar kwanakin ba.
Ya ce duk da kasancewar an kai wannan batu gaban kotu, kuma kotu a amince cewa su ne wakilai da kotun ta amince su gudanar da zaben fitar da ’yan takarar Gwamna da saura mukamai, amma uwar jam’iyyar ta yi watsi da su, ta kawo wasu karfi da yaji suka maye gurbensu.
Mallam Yakubu ya ce suna ji, suna gani aka nada ’yan takara ba tare da amincewar wakilan ba .
“daukacin ’yan takarar da suke tare da tshon mukaddashin Gwamna an hana su yin takara, wadannan ’yan takara sun hada da tsohon Gwamna Jihar Mista Jolly Nyame da sanata Abubakar Tutare dan majalisar wakilai ta kasa, Misat Jerry monwe,” inji shi.
’Yan majalisar dokokin jihar wadanda ke tare da Garba Umar su ma an hana su yin takara. Amma sanata Emmanuel Bwacha dan majilisar wakilai mai wkiltan Bali da Gassol da kuma takwaransa mai wakiltar Ibbi da Wukari an bar su, su yi takara da yake suna tare da bangaran su Darius.
Ya ce wannan rashin gaskiya tare da kin umurnin kotu shi yasa yan takara na mukamai da daban tare da dubban magoya bayan jam’iyyar daukar matakin canja sheka zuwa wata jam’iyya.
Wata majiya ta shaida wa wakinlinmu kwana biyu kafin uwar jam’iyyar ta gayyaci wakilan zuwa Abuja, Shugaba Goodluck Jonathan ya gayyaci tsohon mukaddashin Gwamna Jihar Alhaji Garba Umar zuwa fadar sa, inda ya shaida wa masar cewa dole ya yi watsi da burinsa na takarar Gwamna .
Majiyar ta bayyana cewa Shugaba Jonathan wanda ke kan matsin lamba daga wurin Janar T.Y. Danjuma, cewa dole ne ya hana Garba Umar takara, ya maye gurbinsa da yaronsa, Mista Darius Ishaku, haka aka yi, inda Jonathan ya ce don tausayi an ba Garba Umar dama ya yi takarar kujerar dan majalisar dattawa ta Arewacin Taraba.
Garba Umar, wanda bai da wani zabi dole ya amince da wannan canji, amma inda gizo ke sakar yadda shi Garba Umar zai fito ya shaida wa magoya bayansa, a cewar majiyar.
Wata majiya ta kuma shaida wa jaridar Aminiya cewa daga nan ne magoya bayan ’yan takara, tare da su suka soma tunanin mafita daga wannan matsala da suka samu kansu a ciki.
A cewar wata majiya ’yan takara da aka hana su yi takara suna tunanin cewa dukkan su za su dunguma zuwa jamiyyar APC ko SDP ko kuma PDM, kodayake an ce ra’ayi ya bambanta, masamman tsakanin ’yan siyasar da suka fito daga yankin Arewacin jihar da kuma wadanda suka fito daga Kudancin jihar.
Majiyar ta ce an gudanar da taro tsakanin dan takarar Gwamna Mista Dabid Sabo Kente da Darakta Janar na kamfen din Garba Umar, watau Alhaji Ahmed Yusuf , inda aka ce wai kila shi Ahmed Yusuf ya zama mataimakin Dabid Sabo Kente.
Mista Dabid Sabo Kente ya shaida wa wakililin Aminiya ta waya cewa abin da uwar jam’iyyar PDP ta yi bai yi wa kowa kyau ba, kuma haka din rashin adalci ne.
Ya ce sun mika kukansu ga uwar jam’iyyar don a duba wannan lamari, ya kuma kara da cewa su sun kansace masu biyayya ga jam’iyyar PDP; kuma sun taimaka wa jam’iyyar wajen samun nasara a zabuka daban-daban fiye da shekaru 10, amma ga irin rashin adalcin da aka yi musu.
Mista Dabid Kente ya ce za su koma wata jam’iyya muddun uwar jam’iyyar ba ta canja matsayin ta na hana gudanar da zaben ’yan takara, kamar yadda doka ta jam’iyyar ta tanadar ba.
Ya ce a yau 17 ga watan Disamba ne ya kamata a warware wannan badakala, domin ranar ce hukumar zabe za ta rufe karbar sunayen ’yan takara.
Ya ce ga dukkan alamu jam’iyyar PDP za ta fadi zabe a jihar muddin an ki yin adalci ga dukkan ’yan takara da sauran magoya bayan jam’iyyar a jihar.
Alhaji Ahmed Yusuf bai dauki wayar wakilinmu ba, wanda ya nemi ya ji ta bakin sa kan wannan lamari.
Ita ma sanata Aisha Jummai Alhasan ’yar takarar Gwamna a karkashin jam’iyyar APC, wadda ake zargin cewa wai tana da hannu kan wannan lamari ba, ta amsa kiran wakilinmu da ya yi mata don jin ta bakinta kan wannan lamari ba.
Wannan danbarwar siyasa ta kara kawo zaman dar-dar ga jama’ar jihar, inda jita- jita ke ta tafiya, sannan kuma an fuskanci rashin jituwa tsakanin matasa magoya bayan wasu daga cikin ’yan takara a garuruwa Jalingo da Wukari da Takum a yan kwanakin nan.