A ranar Laraba ne, Allah Ya yi wa xan tsohon gwamnan Jihar Legas, kuma jigo a Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu mai suna Jide rasuwa.
An samu labarin rasuwar ne a wani shafin twitter mai suna APC United Kingdon chapter, inda suka wallafa cewa “Muna bakin cikin sanar wa Najeriya cewa Mista Jide Tinubu, xan shugabanmu a jam’iyya @AsiwajuTinubu ya rasu. Allah Ya jikanshi.”
Shi dai Jide, ya karanci shara’a ne a Jami’ar Liverpool, da ke Ingila. Kuma ya zama qwararren lauya a shekarar 1999.