✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (9)

Har zuwa karfe 10:30 na dare, Alhaji Baba da uwargida Farida ba su samu sasanci da juna ba. Ya yi kokari, ya yi markabun duniyar…

Har zuwa karfe 10:30 na dare, Alhaji Baba da uwargida Farida ba su samu sasanci da juna ba. Ya yi kokari, ya yi markabun duniyar nan amma ya kasa shawo kanta. Ya ma rasa abin da ke masa dadi a rayuwa. Ya samu wuri can daga gefen kujera ya zauna, ya yi wani uban tagumi, yana tunanin zuci. Ita kuwa Farida, tun lokacin da ya shigo gidan nan ya same ta, haka take har zuwa lokacin. Ba ta matsa nan da can ba, tana zaune cikin murtukakkiyar fuska, kamar hadarin da ke shirin zubar da ruwa.

“Gaskiya wannan al’amarin ya ishe ni haka nan!” Abin da Baba ya fada ke nan cikin wata kakkausar murya, tare da matsanancin bacin rai, kamar wanda aka watsa wa tafasasshen zuwa. Ita kuwa Farida ba ta ma san yana yi ba, ko kallon shiyyarsa ba ta yi ba.

“A tsawon rayuwar aurenmu, ban taba shiga irin wannan yanayin ba.” Ya ci gaba da magana cikin izza da bakin rai. “Saboda me za ki zabi wannan yanayi na kunci da kuntata wa rayuwata? Tun da al’amarin nan ya fara, na titsiye ki domin ki gaya mini laifin da na yi miki kin kiya. Na tambaye ki, shin akwai rana guda da na taba uzzura miki ko na ci zarafinki, ko na wulakanta ki? Shin akwai ranar da na gaza sauke nauyin da Allah Ya dora mini a matsayina na mijinki, a gare ki ko ga ’ya’yan da Allah Ya ba mu? Akwai lokaci daya da na ci mutuncin wani naki, na kusa ko na nesa? Shin daidai da rana guda, ko za ki gaya mini, lokaci guda da na gaza ba ku ci da sha da sutura?”

Har yanzu dai ba ta ce uffan ba, shi kuwa ya ci gaba da zuba kamar kanyar da ba zaki. Kan haka ne, ’yarsu da suke kira da suna Hajajju ta fito daga daki cikin firgici.

“Baba, baba…lafiya kuwa?” Hajjaju ta tambaya, fuskarta cike da damuwa.

“Babu damuwa, ki koma daki ki ci gaba da barcinki. Wannan al’amari ne tsakanina da mahaifiyarku. Za mu daidaita komai.”

Ya tashi tsaye ya kama hannunta, ya mayar da ita daki, ya sanya hannu ya jawo kofar ya rufe, sannan ya dawo falon. Sai dai duk da wannan bambami da yake, har yanzu Farida ba ta kula ta tasa ba. Nan ya buga wani uban tsaki, ya tashi ya shiga dakinsa, ya bar ta nan zaune.

Farida ta tashi, ta shiga nata dakin, inda bayan ta kintsa, ta kwanta a gadonta, bayan ta yi addu’o’in da ta saba. Ta karanta Ayatul Kursiyya, sannan ta biyo da kafa uku-uku na surorin Ikhlasi, Nas da Falak. Tana gama karantawa sai ta tofa a hannuwanta ta bi dukkan jikinta ta shafe.

Farida ta kwanta barci, zuciyarta cike da sake-sake da zullumin cewa mijinta zai kara aure. Shin wace ce zai aura? Bayan an yi auren, yaya dangantaka za ta kasance? Shin anya za ta samu natsuwa da kishiya ko kuwa? Anya ba wannan ne sanadiyyar rabuwar aurenta da Alhaji Baba ba?

***

“Ke munafuka, algunguma…daga rana mai kamar ta yau, ba za ki kara marmarin zama gidan nan ba!” Wata mummunar tsohuwa ce sanye da bakaken kaya take gaya wa Farida haka.

“Da ke nake, ko ba ki ji na!” Tsohuwar ta ci gaba da fadin haka, jikinta na tsuma kamar ana kada mata gangi. “Daga ranar nan, ke da wannan mijin naki sai dai a Lahira!”

Farida ta yi tsuru-tsuru, tana cikin tsoro da firgici. Ba ta ankara ba tana ja da baya, har ta kai kanta kuryar daki. Ta rasa hanyar da wannan hatsabibiyar mata ta shigo. Matar ta rika biyo ta tana zazzare mata idanu. Lokacin da ta zo kusa da ita sai ta ga ta tsaya. Ta daga hannunta na hagu sama.

“Yaaa Kantankali namijin aljanu, kai nake kira ba wani ba. Ga bukatata nan, jefo mini dukkan sinadaran yakar wannan algungumar!” Tana rufe baki sai Farida ta ga wani koko ya sauka daga sama zuwa kan yatsun hannun tsohuwar nan na hagu. Ta ga alamar cewa akwai wani bakin ruwa mai kauri da ke cikin kokon. A lokaci guda kuma sai ta ga wani sharbeben takobi ya sauko a hankali, ya cake a cikin kokon.

Farida ta gama firgicewa, ta samu kanta tana furta kalmomin istirja’i. “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Hasbunallahu wa ni’imal wakil!”

Tsohuwar nan ba ta kara cewa komai ba. Ta sauko da kokon nan kasa, ta sanya hannu ta zare takobin daga kokon. Ta dauki kokon nan ta watsa ruwan da ke cikinsa ga Farida. Ita kuwa ta buga wata irin kuwwa. Kafin ka ce wani abu, tsohuwar nan ta nufo wajenta da takobin nan da nufin sarar ta. Ita kuwa Farida ta yi wani gwauron tashi, ta bazama da gudu. Ta banke kofa ta fita daga dakin da gudu. Tsohuwa kuwa ta ce da wa aka hada ta, ba da ita ba? Ta bi ta da gudu da takobi zare a hannu.

“Allahu Akbar, Allahu Akbar!” Wannan kiran Sallah da ladanin masallacin unguwar ya fara, shi ne ya farkar da Farida daga barci.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Ashe mafarki ne nake yi. Ya Allah Ka yi mini jagora, Ka cece ni daga dukkan sharri!

Za mu ci gaba