✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (18)

A ci gaba da wannan labari, a makon jiya mun tsaya ne daidai inda aka ce: “Na farko dai Allah Ya albarkace ku da ’ya’ya,…

A ci gaba da wannan labari, a makon jiya mun tsaya ne daidai inda aka ce: “Na farko dai Allah Ya albarkace ku da ’ya’ya, ke ce uwargida kuma kin tabbata mijinki yana kaunarki. Ga shi dai Allah Ya huwace wa mijinki arziki. Yana da sana’a, yana da mutunci kuma yana da ilimin bautar Allah daidai gwargwado. Idan kika kwantar masa da hankali, kika bi shi sau da kafa, Allah zai taimake ku gaba daya. Ko kuwa yaya kika gani, yayarmu?” Ya fadi haka, a lokacin da ya kura wa Yaya idanu. Ga ci gaba:

 

A karo na uku ke nan Saratu tana neman lambar wayar kawarta Binta amma ba ta samu ba. Abin da na’ura ke gaya mata shi ne, wayar a kashe take. Amma duk da haka ta ki hakura, domin kuwa tana matukar bukatar yin magana da kawar tata, saboda abin da ke damunta. A karo na hudu, ta sake danna maballin da ya kawo mata da lambarta, ta sake dannawa, amma sakon da aka gaya mata bai canja ba.

“Kash!” Abin da ta fada ke nan cikin damuwa, bayan ta buga wani uban tsaki. “Ai kuwa Binta ba ta rufe wayarta, me ya faru yau? Lallai ne kuwa in gana da ita yau, domin abin da ke ci mini rai, ita kadai ce za ta iya ba ni shawarar da ta dace.”

Saratu ta ci gaba da korafi ita kadai kamar wacce ke shirin zautuwa. Da ta gaji da buga waya ba ta samu biyan bukata ba, sai ta jefar da ita gefe guda, ta fuskanci wani abin na daban. Ta shiga cikin damuwa ne, kasancewar yau kwana uku ba ta gana da sahibinta, Alhaji Baba ba. Rabon da ta sanya shi a ido, tun ranar da suka halarci bikin ranar haihuwar Binta. Ta buga masa waya ya fi a kirga amma bai dauka ba sai sau daya. Shi ma kafin ya dauka, sai da ta yi nacin bugawa fiye da sau goma. Bayan ya dauka, maganar da suka yi duka ba ta wuce sakan goma ba. “Ki yi hakuri, ina cikin wata damuwa; zan kira ki.” Abin da ya fada ke nan, kafin ya kashe wayarsa.

Tun daga lokacin nan, ba ta sake samun sukuni ba har sai da ta yi ta bincike. Hasali ma, sai da ta yi zarya fiye da kima zuwa shagonsa na Kantin Kwari amma ba ta samu ganinsa ba. A wannan hakilon nata ne ta gano cewa lallai babu lafiya ne a gidansa. Ta samu labari daga majiyarta cewa, shi da matarsa ne suke sa-in-sa, har ma ta yi yaji. Abin da ya kara tada mata da hankali shi ne, labarin da ta jiwo cewa wannan tata-burza, ita ce ta haddasa ta.

Tana zaune sai ta yi zumbur ta tashi, ta nufi dakin mahaifiyarta, inda ta debi ruwa a kofi ta kwankwada. Ta dawo dakinta ta zauna. Tana zama sai ta rarumi wayarta, ta sake lalubo lambar kawarta ta danna maballin kiranta. A wannan karon, kira daya sai ta ji layin a bude. Nan take ta buga doguwar ajiyar zuciya.

“Aloooo, kawalli! Kina neman saka mini ciwon zuciya.” Abin da ta fada ke nan, lokacin da ta ji muryar Binta.

“Haba dai, me ya yi zafi haka shi ba wuta ba?”

“Wallahi, ni a yadda nake ji, wannan matsalar tawa ai ta fi wutar ma zafi. Ina matukar son ganinki.”

“Subuhanallahi! Ba dai wani ne ya mutu ba ko?” Binta ta tambaya.

“Babu wanda ya mutu, ke dai idan kina gida, bari in zo yanzu in same ki. Maganar nan ba ta waya ba ce, mai tsawo ce. Matsaloli biyu ne ke ci mini rai kuma ke ce kadai za ki iya ba ni shawarar da ta dace.”

“Ina gida, sai kin zo.”

“Madalla, ga ni nan zuwa.” Saratu ta nisa, sannan ta kashe wayar. Ba ta bata lokaci ba ta shirya ta fita daga gidansu, ta yi wa gidan su Binta tsinke.

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

 

Ya ku masu bibiya tare da aiko sakonni a wannan fili! Ina yi muku gaisuwa da jinjinar jimirin bibiya. Haka kuma ina ba ku shawarar ku rika turo sakonninku ta WhatssApp (08020968758) ko ta I-Mel, [email protected] Haka kuma ku rika sanya suna da adireshi da lambar waya a kasan sakon, idan kuma ba ku son a saka lambar wayarku a jarida, sai ku sanar. Har yanzu dai muna kara tambaya, wane gida kuke, GIDAN UWARGIDA FARIDA KO GIDAN AMARYA SARATU? Allah Ya sa mu dace. A wannan makon kuma ga wasu daga cikin sakonninku, kamar yadda aka saba:

 

Daga Rabi’u Muhammad Minjibir-Kano (09019281209):

Salam, Malam Bashir Yahuza, barka da yamma, yaya aiki? Na taba aiko maka da tes dangane da Labarin Malam Shagalalle, nake tambayar ko labarin nan akwai littafi ne wanda ka rubuta, ko a jarida ka haska wannan a Sinadarin Rayuwar? Ka taimaka min da amsa. Kuma ina mai ba da shawara kan a buga shi ya zama littafi, domin jaridar ba ta isa kauyuka da yawa.  Na gode, Allah Ya kara wa alkalaminka tawada.

 

(Madalla, Malam Rabi’u, wannan labari na Malam Shagalalle, a nan shafin ne kawai aka wallafa shi, amma ba a samar da shi a littafi ba, mai yiwuwa sai nan gaba idan Allah Ya ba da iko. Na gode kwarai da kulawa. – Bashir Yahuza Malumfashi)

 

Daga Aminu Ahmed Kazaure:

Ina fata wannan filin na Dausayin Kauna zai isar mini da sakona ga masoyiyata, abin kaunata wato Hannatu Ibrahim.

 

Daga Abdulhannan Potiskum (08163282435):

FDK, ina mana fatar alheri gaba daya. A gaskiya ni kam ina gidan Uwargida Farida kuma don Allah FDK wai babu wata kafar sadarwa da za mu rika samun ci gaban Labarin Farida na shafin Dausayin Kauna, kamar su WhatsApp, Facebook, Tweeter da sauransu? Saboda karancin lokaci na samun karanta jaridar Aminiya da zuwa wurin sayen jaridar. Ka huta lafiya!

 

Daga KSK Khalifa  Pandogari:

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta so! Son mai sonka ya fi ka ba shi kudi.

 

Daga Amina Sabi’u Waziri Bauchi:

Asalamu alaikum Shugaba FDK, da fatar kana lafiya. Allah Ya kara lafiya. Ina mika gaisuwa zuwa ga FDK, ina jin dadin kasancewa da ku.

 

Daga Babel el-Hussain:

Amincin Allah ya tabbata a gare ka Sarki Mai FDK, da fatar kana lafiya; ya yakokari, yaya aiki? Allah Ya kara maka hakuri da mutanen wannan shafi. Sannan ina mika sakon gaisuwa zuwa wajen abokan wannan dandali. Allah Ya bar mu tare. Ina mika muhimmiyar gaisuwa a gare ku masoyan wannan shafi na Dausayin Kauna.

 

Daga Rabi’u Baban Ustaz:

Ina bibiyar wannan shafin mai albarka. FDK, ban taba aiko da sako ba sai a wannan karo. Don Allah FDK cigiya zan ba ka, ina neman budurwa wacce za mu yi soyayya ta gaskiya ta kai mu ga aure; in dai tana sona, za ta yi hakuri da talaucina da rashin kyauna, ina sonta a duk inda take; komai muninta.

 

Daga Yasira Umar Legas (08162457251):

FDK da fatar kana lafiya, Allah Ya sa haka amin. a gaskiya ina gidan Alhaji Baba da ya kara aure idan dai zai yi adalci a tsakaninsu, domin namiji daya ba a yi shi don mace daya ba.

 

Daga Sani Kebbi (07032922021):

Dausayin Kauna, ni dai kam ina tare da Alhaji, ina goyon bayan ya kara mata amma ba irin Saratu ba mai kai shi wurin fati amma kada ya tsaya da mata guda, mata guda ciwo ce.

 

Bashir Shu’aibu Kara (08034766200):

Abin mamaki yadda mata yanzu ba su tsoron zawarci, inda za ka ga yarinya ba ta jimami idan aka ce igiyar aure tana rawa; sai ka ga ko a jikinta.

Za ka ga yarinya kafin ta yi aure komai kankantar gari akalla ka samu zawarawa biyar a unguwar, dama watakila tana sayar da abinci tana samun kudi sosai; har ta kai ba ta sha’awar aure. Ko kuma tana karatu aka yanke aka yi aure, lokacin da take karatu tana da burinta a rai da take so ta zama kafin ta yi aure.Saboda haka duk soyayya da ake wa juna sai ka ga ta zama kiyayya.

Haka shi ma bangaren miji, duk yadda suke soyayya da, yana samun kudi sosai tunda dama abin da yake samu kila ba zai iya biyan bukatunta ba amma soyayya ta sa ba zai iya barinta, sai ya yi iya yinsa a yi aure, daga karshe abubuwa sun fara yawa sai fushi, bacin rai, sai kiyayya ta fara shiga. Ita macen sai ta dawo gida ta ci gaba da sha’aninta, tamkar yadda take a da, da mu’amala da mutanen layi.