A jibi Lahadi, 26 ga wannan wata ne za a yi wasa a tsakanin kulob din Manchester United da na Chelsea a gasar rukunin firmiya na Ingila.
Za a yi wasan ne da misalin karfe biyar na yamma agogon Najeriya a filin wasa na Manchester watau Old Trafford.
Wasa ne da ke da muhimmanci ga dukkan kungiyoyin biyu musamman ganin cewa idan United ta samu nasara za ta karya lagon Chelsea a kakar wasa ta bana don kawo yanzu babu wata kungiya da ta samu nasara a kanta a gasar. Ta yi nasara a wasanni bakwai daga cikin takwas inda ta yi kunnen doki sau daya kuma ta hada maki 22. Yanzu haka ita ce kan gaba a teburin gasar a Ingila.
Ita kuwa Manchester United idan ta kuskura aka doke ta ko shakka babu za ta yi kasa a teburin gasar. Yanzu haka ita ce ta shida bayan ta hada maki 12 daga cikin wasanni 8.