A ci gaba da gasar Firimiya ta Ingila a jibi Lahadi ake sa ran za a yi Karon-Battar Birnin Landan a tsakanin kulob din Arsenal da Chelsea.
Wasan zai gudana ne a filin wasa na Arsenal da ake kira Emirates da misalin karfe uku na rana agogon Najeriya.
Kamar yadda jadawalin gasar ya nuna, wannan ne wasa mafi zafi a wannan mako kuma shi ne wasa karo na 20 bayan da aka fara gasar.
Wannan ne wasa na biyu da sabon kocin Arsenal Mikel Arteta zai jagoranta.