Ga wasu muhimmin abubuwa kan tsohon Ministan Abuja a zamanin Abacha, Laftanar-Janar Jeremiah Timbut Useni (murabus) wanda ya rasu bayan fama da jinya.
- An haifi Jeremiah Timbut Useni ne a ranar 16 watan Fabrairu, 1943.
- Ɗan asalin ƙabilar Tarok ne a Karamar Hukumar Langtang da ke Jihar Filato.
- Ya shiga aikin soja tun yana ɗan shekara 14 a duniya, inda ya fara makarantar yaran soji (NMS) da ke Zariya.
- Abokansa na kiran shi da laƙabin Jerry Boy, kasancewansa abokin tafiya nagari kuma mai haba-haba da jama’a.
- Shi ne tsohon Gwamna tsohuwar Jihar Bendel na mulkin soja daga shekarar 1984 zuwa 1985.
- Ya kasance tsohon Ministan Sufuri a zamanin mulkin soji.
- Ya riƙe muƙamin Kwata Masta-Janar na Rundunar Sojin Najeriya.
- Shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya daga 1993 zuwa 1998, zamanin tsohon shugaban mulkin soja Marigayi Janar Sani Abacha.
- A zamanin mulkin farar hula ya shiga siyasa kuma ya lashe zaɓen Sanata mai Wakiltar Mazaɓar Filato ta Kudu a Kudu a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.
- Ya rasu ranar Alhamis 23 ga watan Janairu, 2025 yana da shekara 83.