A makon nan ne ’yan wasa da yawa ke buga wa tawagoginsu wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya ko kuma karawar sada zumunta.
Haka kuma a karshen makon ake sa ran ci gaba da wasannin manyan gasar Turai, sai dai kawo yanzu Robert Lewandowski na Bayern Munich ke kan gaba da kwallo 31 a raga.
Shi ne ke jan ragama a jerin wadanda suka zura kwallaye da yawa a manyan gasar Turai a kakar bana.
Manyan gasar Turai sun hada da Firimiyar ta Ingila da La Liga ta Sifaniya da Bundesliga ta Jamus da Serie A ta Italiya da kuma Ligue 1 ta Faransa.
Dan wasan Bayern Munich ya buga gasar Bundesliga 27 kuma ya ci kwallo 31, ya bayar da daya aka zura a raga da katin gargadi biyu.
Dan wasan tawagar Poland, mai shekara 33 ya buga wa Bayern da kasarsa wasa 48 ya kuma ci kwallo 58, ya bayar da takwas aka zura a raga a kakar bana.
Dan kasar Faransa, Karim Benzema ke biye da shi a yawan zura kwallaye a manyan gasar Turai, mai 22 kawo yanzu.
Mai taka leda a Real Madrid, ya buga wasa 25 a La Liga da cin kwallo 22 ya kuma bayar da 11 aka zura a raga.
Ciro Immobile mai kwallo 21 a Serie A a bana, shi ne na uku sai Mohamed Salah na Liverpool mai kwallo 22 a wasa 25, ya bayar da 10 aka zura a raga.
- Robert Lewandowski — Bayern (31)
- Karim Benzema — Real Madrid (22)
- Ciro Immobile — Lazio (21)
- Mohammed Salah — Liverpool (20)
- Patrik Schick — Leverkusen (20)
- Dusan Vlahovic — Fiorentina (17)
- Wissan Ben Yedder — Monaco (17)
- Martin Terrier — Rennes (16)
- Ering Haaland — Borrusia Dortmund (16)
- Giovanni Simeone — Verona (15)