Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu zai tafi Abidjan, Babban Birnin Kasar Côte d’Ivoire don mara wa tawagar ‘yan wasan Super Eagles baya.
Najeriya za ta kara da masu masaukin baki, Côte d’Ivoire a wasan karshe na Gasar Nahiyar Afirka (AFCON 2023), da za a yi a ranar Lahadi.
- PDP ta lashi takobin lashe zaben kananan hukumomi a Gombe
- Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 4, sun ceto mutum 11 a Kaduna
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika (CAF) Patrice Motsepe ne, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abidjan a ranar Juma’a.
Super Eagles ta lallasa Afrika ta Kudu a wasan kusa da na karshe a bugun fanareti, da ci 4 da 2.
Najeriya za ta fafata da Côte d’Ivoire a filin wasa na Alassanne Ouattara da ke Ebimpe a Abidjan.
Za a take wasan da misalin karfe 9 na dare, agogon Najeriya.
Najeriya dai ba ta yi rashin nasara ko daya ba tun da aka fara gasar.
Kazalika, tawagar ‘yan wasan ta doke masu masaukin baki da ci daya mai ban haushi daga hannun dan wasan bayan Najeriya, Troost Ekoong a bugun fanareti a wasannin rukuni.
Tuni dai magoya bayan Super Eagles suka shiga bayyana ra’ayinsu tare da bai wa ‘yan wasan kwarin gwiwa don lashe gasar.