Mujallar Forbes ta wallafa cewar Kylian Mbappe shi ne dan wasan tamaula da yake kan gaba wajen samun kudi a 2022 a duniya.
Karon farko bayan shekara tara da ba a samu ko dai Cristiano Ronaldo ko kuma Lionel Messi a matsayi na farko ba.
- Zaben 2023: Mansurah Isah da Rahama Sadau sun yi musayar yawu
- Ina makomar Sanata Ahmad Lawan a siyasance?
Forbes mai bincike da kididdigar kudi ta yi kiyasin cewar dan kwallon Paris St Germain da Faransa, mai shekara 23 ya samu $128m (£115.2m) a kakar nan.
Mbappe ya kai wannan matakin, bayan da ya saka hannu a PSG kan yarjejeniyar mai tsoka ta ci gaba da taka leda a kungiyar a watan Mayu.
A lokacin an yi ta hasashen cewar Real Madrid zai koma da taka leda.
Takwaran Mbappe a PSG, Lionel Messi shi ne na biyu da ya samu kudin shiga $120m (£108m) sai dan wasan Manchester United, Ronaldo na uku mai $100m (£90m).
Neymar dan wasan PSG da tawagar Brazil, an kiyasta cewar ya samu $87m (£78.4m) a kakar 2022-23 shi kuwa dan kwallon Liverpool Salah da Masar ya hada $53m (£47.7m).
Jerin ’yan wasan tamaula 10 da suka samu kudi mai tsoka a 2022:
- Kylian Mbappe PSG $128m (£115.2m)
- Lionel Messi PSG $120m (£108m)
- Cristiano Ronaldo Manchester United $100m (£90m)
- Neymar PSG $87m (£78.4m)
- Mohamed Salah Liverpool $53m (£47.7m)
- Erling Haaland Manchester City $39m (£35.1m)
- Robert Lewandowski Barcelona $35m (31.5m)
- Eden Hazard Real Madrid $31m (£27.9m)
- Andres Iniesta Vissel Kobe $30m (£27m)
- Kevin de Bruyne Manchester City $29m (26.1m)