A karon farko tun bayan rufe iyakokinta sakamakon barkewar annobar coronavirus, Saudiyya ta gindaya wa wasu kasashen 25 sharuda kafin ta amince ’yan kasashen su samu damar shiga cikinta.
Saudiyya ta shardanta wa ‘yan kasashen yin alkawarin biyan tarar Riyal dubu 500 idan suka saba daya daga cikin ka’idojin.
Babu shakka annobar ta kawo sauyi a fannoni daban-daban na gudanar da harkokin rayuwa, wanda hakan ya sanya aka gudanar da aikin Hajjin bana cikin wani yanayi na sabon salo kuma da mutane tsiraru.
Rahoto da mujallar ‘Life in Saudi’ ta fitar, ta ce daga cikin sharuddan da Saudiyya ta gindaya akwai bukatar tabbatar da dukkan fasinjojin da aka dauko daga kasashen ba sa dauke da kwayar cutar.
Ga sharudan da Saudiyya ta gindaya wa fasinjojin kasashe 25
- Kowane fasinja ya kasance ba ya nuna wata alamar matsalar numfashi ko hanta ko wata alama da ke nuna yana dauke ko ya kamu da cutar korona.
- Dole ne duk wani fasinja ya killace kansa na tsawon kwana bakwai idan ya shiga Saudiyya.
- Akwai bukatar kowane fasinja ya sauke wata manhajar mai suna ‘Tataman Application’ cikin sa’o’i takwas wadda za ta nuna wurin da ya sauka, kuma ba zai samu damar barin wannan wuri ba har sai ya cika kwanaki bakwai a killace matukar ba matsalar lafiya ce ta taso ba.
- Dole ne kowane fasinja ya shiga cikin mahanjar domin shigar da bayanan yanayin da yake ciki.
- Haka kuma dole ne kowane fasinja ya amince zai biya tarar Riyal dubu 500 a yayin da aka same shi da karya daya daga cikin dokokin kuma zai yi zaman gidan yari na shekaru biyu.
Ga jerin kasashen da aka gindaya wa wadannan sharudan
- Najeriya
- Sudan
- Afirka ta Kudu
- Kenya
- Habasha
- Philippines
- Bangladesh
- Kuwait
- Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)
- Masar
- Oman
- Faransa
- Jamus
- Tunisia
- Birtaniya
- Lebanon
- Morocco
- Italiya
- Sin
- Turkiyya
- Austria
- Girka
- Indonesia
- Bahrain
- Malaysia