Gwamnatin Tarayya ta haramtawa wasu jami’o’in ƙetare 18 tafiyar da harkokinsu a Najeriya tana mai bayyana su a matsayin masana’antun haɗa digiri.
Gwamnatin ta kuma gargaɗi ’yan Najeriya da su guji shiga jami’o’in.
- Taurarin Zamani: Mustapha Magaji Mijinyawa (Badaru Dadin Kowa)
- EFCC ta gayyaci tsohuwar Ministar Jin-ƙai Sadiya Farouq
Matakin ya shafi jami’o’i biyar daga Amurka sai guda shida daga Birtaniya, uku kuma daga Ghana.
Da take bayyana matakin dakatarwar cikin wata sanarwa, Hukumar Kula da Jami’o’in Najeriya, NUC ta yi bayani cewa jami’o’in 18 ba su da sahalewar gwamnati don tafiyar da harkokinsu saboda haka ta rufe su.
Ta ce “Hukumar NUC na sanar da jama’a musamman iyaye da ɗalibai cewa waɗannan jami’o’in ba su da lasisin Gwamnatin Tarayya don haka an rufe su saboda take Dokar Ilimi ta Najeriya ta 2004.
A jiya Talata ne Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ce ta dakatar da tantance shaidar digiri daga jami’o’in Benin da Togo, a wani yunƙuri na tsaftace ɓangaren ilimin, har zuwa lokacin da za ta kammala bincike a kan ingancin makarantun.
Wannan lamari dai na zuwa ne bayan wani rahoton binciken ƙwaƙwaf da Jaridar Daily Nigerian ta yi a baya-bayan nan, inda ta ce wani wakilinta da ya yi ɓad-da-kama ya samu takardar shaidar digiri daga wata jami’a a Jamhuriyar Benin a cikin mako shida kacal.
Jerin jami’o’in ƙetare 18 da haramcin ya shafa:
1. University of Applied Sciences and Management, Port Novo ta Jamhuriyyar Benin.
2. Volta University College, Ho, Volta Region, Ghana.
3. The International University, Missouri, USA da ke da cibiyoyi a Kano da Legas.
4. Collumbus University, UK.
5. Tiu International University, UK.
6. Pebbles University, UK.
7. London External Studies UK.
8. Pilgrims University.
9. West African Christian University.
10. EC-Council University, USA, da ke da cibiya a Ikejan Jihar Legas.
11. Concept College/Universities (London) da ke Ilorin.
12. Houdegbe North American University.
13. Irish University Business School London.
14. University of Education, Winneba, Ghana.
15. Cape Coast University, Ghana.
16. African University Cooperative Development da ke Kwatano a Jamhuriyyar Benin.
17. Pacific Western University, Denver, Colorado da ke da cibiya a Owerri.
18. Evangel University of America and Chudick Management Academic da ke Legas.