✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta gayyaci tsohuwar Ministar Jin-ƙai Sadiya Farouq

Sadiya Farouq ta musanta zargin hannu a badaƙalar da ake zarginta.

Tsohuwar Minista a Ma’aikatar Jin-ƙai, Sadiya Umar Farouq, za ta bayyana a gaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), bisa zarginta da hannu a badaƙalar fiye da naira biliyan 37 da miliyan 170.

Bayanai sun ce a makon jiya ne hukumar ta aika wa tsohuwar ministar goron gayyata sakamakon wani bincike da ta ƙaddamar a kan aikace-aikacen ma’aikatarta lokacin da take riƙe da muƙamin tsawon shekara shida.

Ana binciken Sadiya Farouq wadda ta riƙe muƙamin ministar jin-ƙai a gwamnatin Muhammadu Buhari kan zargin hannu a badaƙalar halasta kuɗin haram na fiye da naira biliyan 37 da miliyan 170, da wani ɗan kwangila James Okwete ya aikata.

Wata majiya a EFCC ta shaida wa BBC cewa babu shakka hukumar ta gayyaci tsohuwar ministar amma ba ta yi wani ƙarin haske ba.

A Litinin din makon jiya ce Sadiya Umar Farouq ta fitar da wata sanarwa tana musanta zargin hannu a badaƙalar da ake zargin James Okwete da aikatawa, inda ta jaddada cewa ba ta ma san mutumin da ake magana a kansa ba.

Jaridar Punch ta ce tuni hukumar EFCC ta gayyaci ƙarin jami’ai da suka yi aiki da Sadiya don samun ƙarin haske a kan yadda ma’aikatar ta tafiyar da al’amuranta a cikin shekara shida.

A makon nan ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIPA), Halima Shehu kan zargin almundahana.

Tinubu ya dakatar da ita ne a ranar Talata kan zargin aikata zamba a hukumar, inda ya maye gurbinta da Mista Akindele Egbuwalo a matsayin mukaddashi har zuwa lokacin da za a kammala bincike.