Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya ce adawar masu adawa ba za ta hana kamfanin jirgin saman Najeriya (Nigeria Air) fara aiki watan Disamba mai zuwa ba.
Sirika ya bayyana wa manema labarai haka ne jim kadan bayan ganawarsu ranar Laraba a Abuja da Kwamitin Majalisar Dattawa kan sufurin jiragen sama da sauran masu ruwa da tsaki a fannin.
- Jonathan ya yi bikin ranar haihuwar wa matarsa da ta mutu
- NAJERIYA A YAU: Shin Da Gaske Peter Obi Ya Jingine Yakin Neman Zabensa?
Ya ce babu gudu, babu ja da baya dangane da fara aikin kamfanin jiragen a Disamba mai zuwa kamar yadda aka ayyana.
“Nigeria Air kamfani ne mai rajista wanda dokar kasa ta san da zamansa, kuma zai soma aiki da yardar Allah,” in ji shi.
Ya kara da cewa, tsakanin yanzu zuwa watan Disamba ake sa ran jirgin ya fara aiki, tare da kyautata zaton yin gogayya da takwarorinsa.
Ministan ya ce, jiragen za su fara aiki ne ba da zummar takura wa kowace sana’a ba, sai don taimakawa wajen bunkasa harkoki da kuma samar da aiki ga ’yan kasa.