✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jayayyar sarautar wakilin gari ta lafa a tsakanin Hausawan Apata

A ranar Talata ne Sarkin Hausawan Apata, kusa da birnin Ibadan, Alhaji Sahabi Sulaiman, ya jagoranci jama’arsa da suka yi addu’o’in godiya ga Allah (SWT)…

A ranar Talata ne Sarkin Hausawan Apata, kusa da birnin Ibadan, Alhaji Sahabi Sulaiman, ya jagoranci jama’arsa da suka yi addu’o’in godiya ga Allah (SWT) da yasa suka shawo kan matsalar rikicin mukamin mataimakinsa (Wakili),  ba tare da kazancewa ba. An yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’in rokon Allah ya kawo karshen matsalolin da kasar nan ke fama da su dangane da tabarbarewar tsaro.
Cikin jawabin da Sakatarensa Alhaji Aliyu Salau Zamfara, ya karanta a madadinsa, Sarkin Hausawan na Apata, ya jinjina wa Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, a game da hanzarta daukar matakin tsoma baki a matsayinsa na Uban jama’a da ya kawo karshen wannan matsala cikin kankanen lokaci. Ya ce, “yanzu mun kawo karshen wannan matsala bayan karbar takardar shaida daga hannun Sarkin Hausawan Ibadan, wanda ya nuna amincewarsa da nadin Alhaji Mu’azu Muhammed, a matsayin mataimaki na wato, Wakilin Gari. Abin da nake bukata shi ne hadin kai da goyon bayanku da zai taimaka mini wajen gudanar da jagoranci bisa adalci da kwatanta gaskiya.”
daya daga cikin ‘yan majalisar Sarkin, Alhaji Haruna Mai Agogo, ya ce, tun farko an samu rashin jituwa a tsakanin mu yamu ne saboda aikin shaidanu da suka yi kokarin raba kawunan jama’a. “Sarki Sahabi Sulaiman, mutum ne da ya samu kyakkyawar shaida, musamman wajen kwatanta gaskiya a cikin al’amuransa, kuma ya dogara da sana’arsa ta leburanci ne ba tare da kwadayin abun hannun mutanensa ba. Shi ne ya tashi tsaye don ganin harkokin kasuwanci sun bunkasa a tsakanin mutanensa da kyautata zamantakewar jama’ar gari. Yanzu haka ya fara fafutikar ganin an kebe wa jama’arsa gurabe da shaguna a cikin sabuwar kasuwar da mahukumta suka gina da za a yi bikin bude ta a watan gobe. Saboda haka ya kamata mu tashi tsaye wajen bayar da gudunmawa da hadin kai domin ya cimma buri.”
daya daga cikin masu adawa a rikicin sarautar, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa, “dole ne mu amince da wannan hukunci, tunda Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Mai Yasin ya sanya baki a maganar.”
Ya ce, mun amince da matsayin ne, domin daya daga cikin iyayeen al’umma ya tsawata mana. “Mu duka muna fatan smaun zaman lafiya da kwnaciyar hankali,” inji shi.