✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jason Day ya fice daga gasar Olampik saboda tsoron cutar Zika

Zakaran kwallon Golf na duniya Jason Day ya bayyana ficewarsa daga gasar Olampik da za a gudanar a birnin Rio da ke kasar Brazil saboda…

Zakaran kwallon Golf na duniya Jason Day ya bayyana ficewarsa daga gasar Olampik da za a gudanar a birnin Rio da ke kasar Brazil saboda “damuwa da yiwuwar kamuwa da cutar zazzabin Zika.”
dan wasan kwallon Golf din mai shekara 28 dan kasar Austireliya ya ce, yayin da hadarin kamuwa da cutar karami ne ba ya cikin mutanen da yake shirye ya fafata a gasar saboda “yiwuwar hadari ga samun juna biyu ga matarsa a gaba.”
Ya kara da cewa: “Fafatawa a gasar Olampik zai ci gaba da kasancewa cikin manyan abubuwan da yake so, amma ba zan fifita kwallon Golf ba a iyalina ba.”
Wani fitacen dan wasan Golf din, Roy Mcllroy ma ya fice daga gasar bisa damuwa da kwayar cutar cizon sauro.