More Podcasts
Yau 1 ga watan Mayu ce aka ware a matsayin Ranar Ma’aikata ta Duniya domin jinjina musu bisa rawar da suke takawa wajen kawo cigaban al’umma.
Sai dai yayin da ’yan Najeriya da dama suke kuka da halin ƙuncin rayuwa a kasar, ma’aikata na kan gaba wajen bayyana yadda suka ce suna tagayyara, kuma ayyukan da suke yi babu riba ta wani ɓangaren.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Wahalar Fetur Ke Jigata ’Yan Najeriya
- DAGA LARABA: Me Ya Sa Ake Ƙin Faɗa Wa Mata Wasu Abubuwa Idan Za Su Yi Aure?
Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba yadda rayuwar ma’aikata a Najeriya ke kasancewa da kuma sauyin da suke fatan samu.