✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jarumi Garzali Miko zai angwance ranar Juma’a

Jarumin zai angwance a ranar Juma'a 20 ga watan Agusta 2021.

Jarumi kuma mawaki a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Garzali Mika’ilu, wanda aka fi sani da Garzali Miko zai angwance ranar Juma’a 20 ga watan Agusta 2021.

Tuni jarumai da dama daga cikin masana’antar suka shiga wallafa katin gayyatar daurin auren Garzali Miko a shafukansu na Instagram.

Jarumin zai angwance da amaryarsa mai suna Habiba Umar Dikwa a Jihar Kaduna.

Za a daura auren ne ranar Juma’a da misalin karfe 1:30 na rana, a Masallacin Juma’a na Fajrul Islam da ke kan Titin Makarfi, a unguwar Rigasa da ke  Jihar Kaduna.

Katin daurin auren jarumin
Katin daurin auren jarumin

An shirya shagulgula da suka da hada wasan sada zumunci na kwallon kafa tsakanin kungiyoyi da dama, wanda kungiyar magoya bayan jarumi Ali Nuhu da Janbulo Academy suka fito wasan karshe a ranar Laraba.

Za a buga wasan karshe na gasar kwallon kafar bikin jarumi Garzali Miko a daren ranar Alhamis.

Jarumai masu shiryawa da sauran masu ruwa da tsakai da suka hadar da Ali Nuhu, Mommie Gombe, Abdul Amart Maikwashewa, Ali Gumzak, Shamsu Dan Iya, Kamal S. Alkali, Lawal Ahmad, Isah A. Isah, Dauda Kahutu Rarara, Salisu S. Fulani, Nasir Naba da sauransu na daga cikin wanda suka halarci wajen wasan kwallon.

Dauda Kahutu Rarara da ango Garzali Miko
Dauda Kahutu Rarara da ango Garzali Miko a wajen wasan kwallon bikinsa