✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarirai 200 aka haifa a sansanin ’yan gudun hijirar Binuwai —SEMA

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta ce jarirai 200 aka haifa a sansanonin gudun hijirar da ke jihar Binuwai.

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Binuwai (SEMA) ta ce jarirai 200 aka haifa a sansanonin gudun hijirar da ke jihar Binuwai.

Sakataren ofishin hukumar na jihar, Dokta Emmanuela Shior, ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Makurdi babban birnin jihar, yayin rabon tallafin kayan abinci ga ’yan gudun hijirar.

“Wadannan jarirai su ne aka yi wa rajistar haihuwa a hukumance, watakila saboda iyayensu na tare a sansanonin.

“Amma muna da yakinin ba su kadai ne aka haifa ba, saboda akwai akalla mutane miliyan biyu da ke sansanonin jihar,” in ji shi.

Sai dai ya ce gwamnatin jihar na yin iya bakin kokarinta domin kawo karshen matsalar tsaron da ta ki ci, ta kai cinyewa a jihar.

A don haka ne ma ya ce wasu daga cikin masu ayyukan sa-kai a jihar sun dau alkawarin tallafa wa jami’an tsaro tsare sansanonin a lokutan bukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.