kasar Japan ta bayyana aniyyarta ta samar da rigakafi kan cutar Ebola daga wani maganin mura, a ci gaba da matakan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da kamfanonin hada magunguna suke dauka don kawo karshen cutar.
Sakataren Gwamnatin kasar Yoshihide Suga ne ya bayyana wa manema labarai hakan ranar Litinin, a birnin Tokyo. Inda ya ce kasarsa za ta yi amfani da wani maganin mura, wanda bai kai ga samun amincewar hukumar WHO don a bai wa wasu masu fama da annobar a yankin Yammacin Afirka da cikakken fatan samun waraka daga cutar. Ya ce maganin mai suna, Fabipirabi, wanda kamfanin hada magunguna na Fujifilm Holdings, za a fara samar da shi ba tare da bata lokaci ba. Kuma ya samu amincewar ma’aikatar lafiyar kasar a watan Maris din da ya gabata. Ya kara da cewa bayan sun kammala gwaje-gwajensu sun gano cewa maganin zai iya zama rigakafin Ebola saboda yadda cutar ta yi kama da mura.
Kakakin kamfanin Fujifilm Takao Aoki ya ce sun fara tuntubar jami’ai a Amurka a wani mataki don fara gwajinsa akan cutar Ebola. Kuma ya ce sun shirya sosai, ta yadda idan maganin ya samu nasara, za su iya bai wa kusan majinyata 20,000, a cikin kankanin lokaci.
Hukumar WHO ta ce ta kwashe lokaci mai tsawo tana kokarin gano maganin Ebola tun bayan barkewar annobar a shekarun 1970.Kodayake a watan jiya, hukumar ta bayyana cewa saboda girman wannan annobar ta bana, za a iya amfani da maganin gwaji ba tare da bin jerin matakan da aka saba ba, kafin fara amfani da kowane sabon magani akan al’umma.
Japan za ta mayar da maganin mura na rigakafin Ebola
kasar Japan ta bayyana aniyyarta ta samar da rigakafi kan cutar Ebola daga wani maganin mura, a ci gaba da matakan da Hukumar Lafiya ta…