✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jana’izar mahaifiyar abokin takarar Abba Gida-gida

A yammacin Asabar ne aka guddanar da jana'izar Hajiya Rabi Abdullahi a Masallacin Al-Furqan da ke Kano

Allah Ya yi wa mahaifiyar mataimakin dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar NNPP, Aminu Abdussalam Gwarzo, rasu.

A yammacin Asabar ne aka guddanar da jana’izar Hajiya Rabi Abdullahi a Masallacin Al-Furqan da ke unguwar Nassaarwa a birnin Kano.

Hajiya Rabi Abdullahi mai shekara 88 ta rasu ne sakamakon takaitaccen rashin lafiya.

Marigayiyar wadda tuni aka shirya jana’izarta bisa tsarin addinin Islama ta rasu ta bar ’ya’ya biyu da jikoki 48.

A sakon ta’aziyyarsa, dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusu, ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayiyar, Ya sanya ta a Aljanna Firdausi, tare da bai wa iyalanta hakurin jure rashin.